✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ayyukan Mazabu: Yadda sanatoci da ’yan majalisa ke sace biliyoyin Naira – ICPC

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da dangoginsu (ICPC) ta zargi sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai da sace biliyoyin Naira da sunan ayyukan mazabu.…

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da dangoginsu (ICPC) ta zargi sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai da sace biliyoyin Naira da sunan ayyukan mazabu.

Wani binciken da Hukumar ICPC ta gabatar mai taken “Bincike kan Ayyukan Mazabu,” ya bankado ayyukan mazaba 424 daga shekarar 2015 zuwa 2018 da kuma wasu daga watan Yuni zuwa watan Agusta bana a jihohi 12 da suka hada da da Adamawa da Akwa Ibom da Bauchi da Benuwai da Edo da Enugu da Imo da Sakkwato da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja wadanda hukumar ta ce an sake maimaita su ta hanyar sake kawo su da ba tare da an canja komai ba, hatta ma kamfanonin da aka yi amfani da su da farko su aka sake maimaita sunansu a wajen gabatar da wadannan kwangiloli a karo na biyu.

Rahoton binciken na ICPC, Shugaban Hukumar ce Mista Bolaji Owasanoye, ya sanya masa hannu. Ya kuma yi zargin cewa ’yan majalisar suna yin haka ne da gangan saboda su handame kudaden da ake ba su don yin wadannan ayyuka na mazabu.

Haka kuma an yi zargin an sanya wasu ayyukan mazabu a cikin kasafin kudi da sunan ‘ayyukan tallafin inganta rayuwa.’

“Wadannan ayyukan tallafin inganta rayuwa, wata hanya ce ta yin sama-da-fadi da ’yan majalisa ke amfani da ita, don sun san cewa zai yi wuya a iya bin kadin wadannan ayyuka saboda yadda ake gabatar da su,” inji rahoton.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fadi a watan Nuwamba cewa talakawa ba su amfana da Naira tiriliyan daya da suka narke a cikin shirin ayyukan mazabun da aka aiwatar cikin shekara 10 da suka gabata ba.

“Wannan yana nuna akwai badakala lura da yadda aka kashe makudan kudi kan ayyukan mazabu da kuma ayyukan tallafin inganta rayuwa da suka shafi kananan sana’o’i.

“Misali a shekarar 2015, kudaden da aka ba wa kananan sana’o’i ta hannun SMEDAN sun kai Naira biliyan 1 da miliyan 592 da dubu 323 da 599, ayyukan mazabu kuma sun samu Naira biliyan 5 da miliyan 814 da dubu 369 da 579. Kuma kashi 95 na ayyukan mazabu an yi su ne kan ayyukan inganta rayuwa. Wadannan kudi sun karu a shekarar 2016 zuwa Naira biliyan 11 da miliyan 120 da dubu 99 da 958.

Hukumar ICPC ta fitar da karin bayanai inda a karshe ta ba da shawarar a dakatar da bada kudin ayyukan mazabu na wucin gadi don hana ci gaba da bushasha da dukiyar jama’a.

Duk kokarin jin ta bakin mai magana da yawun Majallisar Dattawa ta kasa, Godiya Akwashiki ya ci tura saboda kin amsa kiran waya.