✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Azumi: Farashin kankana ya rubanya na bara

Kankana na daga cikin kayan marmarin da akan yowa rica a kasuwanni ko wuraren da akan sayar da kayan lambu. Don haka masu azumi ke…

Alh. Sule Sakkwato, dillalin kankanaKankana na daga cikin kayan marmarin da akan yowa rica a kasuwanni ko wuraren da akan sayar da kayan lambu. Don haka masu azumi ke jika makoshinsu da kayan marmarin da suka hada da kankana, amma a bana   aka gani a shekaru biyu baya da suka wuce a kasuwannin sayar da Kankanar, musamman farashinta ya sha bamban da irin yadda ake sayar da ita suka ruba sau uku ko hudu ga farashin baya. Wani falke mai suna Alhaji Sule Sakkwato mai sana’ar sayar da kankanar a jihohin da suka hada da Legas da Abuja da Sakkwato da Kano da sauran masu saya su sayarwa don samun na cefane ya ce, lallai kankana farashinta ya yi tashin gwauron zabo ne saboda karancinta. “A shekaru biyu da suka wuce,ina tura a kalla mota biyar har zuwa goma ta Kankana a jihohin kudu da wasu jihohin Arewa, amma a bana biyu ma sai anyi da gaske kafin a samu,” inji Alhaji Sule. Har ila yau, ya kara da cewa, da ma kananan hukumomin Jibiya da Batsari na Jihar Katsina suka fi noman kankanar a Arewacin kasar nan, sai Jihar Kano dake biye da su, to bana ta kai har shiga suke yi a makwabciyar kasa, wato Jihar Maradi da ke Jamhuriyar Nijar, don farautarta, amma babu ita kamar shekarun baya. dan kasuwar ya ce, da suna sayen guda 100 ta manya akan Naira dubu takwas, a yanzu irinta sai sun saye ta Naira dubu 20 wani lokaci har da doriya.”Kankanar da za a saya Naira 20 yanzu sai an saye ta Naira 150.
Shi kuwa sarkin Lambun Jibiya, Alhaji Bala ya ce, karancin da kankanar ta yi yana da nasaba da karancin ruwan sama. “Ita dai kankana nomanta ba wata wahala ake yi ba sosai kamar na sauran kayan lambu. Inma har za a ce ana kashe kudi masu yawa to bai wuce ga maganin kwari ba, amma babban dai abin da tafi so shi ne, banruwa. To ina ganin wannan karancin ruwan ne yasa ta yin karancin da yasa ta yi tsada”. kamar yadda sarkin lambu na Jibiya Alhaji Bala ya ce. Sai dai sarkin lambun ya ce,nan bada jimawa ba kankanar zata wadata watakila harma tafi na shekarun baya yawa.
Shi kuwa Alhaji Muntari Nepa cewa yayi,in baccin muhimmancin da kankanar take da shi ta fuskar lafiya da sai suce akai kasuwa saboda irin tsadar da tayi musamman acikin wannan wata mai alfarma na Ramadan. Alhaji Muntari yayi kira ga ‘yankasuwa da su rika tausayawa talaka a irin wannan lokaci,su kuma sani cewar ba tsadar da suke yi ba ne zaisa su yi arziki cikin dan lokaci, su nemi albarkar abin yafi.”in ka kyautata kaima sai Allah Ya kyautata maka,” a cewarsa.