✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram ta mamaye kananan Hukumomin Borno 8 – Dan Majalisa

Dan Majalisar wakilan tarayya daga jihar Borno, Ahmadu Jaha, daga mazabun Kananan Hukumomin (Damboa/Gwoza/Chibok) ya ce, mayakan Boko Haram sun mamaye Kananan Hukumomin takwas cikin…

Dan Majalisar wakilan tarayya daga jihar Borno, Ahmadu Jaha, daga mazabun Kananan Hukumomin (Damboa/Gwoza/Chibok) ya ce, mayakan Boko Haram sun mamaye Kananan Hukumomin takwas cikin 10 da ke yankin Arewacin jihar.

Ahmadu, ya bayyana hakan ne a zauren majalisar lokacin da ake tattauna bukatar yadda za a tallafawa jami’an tsaron yankin da wasu kudade da zai taimaka masu.

Dan majalisar ya zargi shirin da ake yi akan yaki da ‘yan Boko Haram, a matsayin wanda babu sahihanci a ciki, saboda har yanzu akwai wasu yankunan da suke hannun mayakan Boko Haram a jihar.