✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a ba mu diyyar harin  jami’an tsaro na Apo Abuja ba – Kamal

Daya daga cikin wadanda harin da jami’an tsaro na DSS da sojoji suka kai wa wadansu masu tuka Keke NAPEP a wani kango a gundumar…

Daya daga cikin wadanda harin da jami’an tsaro na DSS da sojoji suka kai wa wadansu masu tuka Keke NAPEP a wani kango a gundumar Apo a Abuja ya shafa bisa zargin cewa su ’yan Boko Haram ne a watan Satumban 2013, mai suna Kamal Abdullahi ya ce har yanzu su da aka tsare a lokacin da lamari ya faru ba a ba su komai ba, da sunan diyyar da gwamnati ta bayar na Naira miliyan 135.

Kamal  Abdullahi ya bayyana haka ne  lokacin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ce a wannan hari da jami’an tsaron suka kai an rasa rayukan mutum 8 tare da raunata mutum 11, kuma daga baya gwamnati ta biya diyyar Naira miliyan 135, domin a bai wa wadanda wannan al’amari ya shafa.

Kamal Abdullahi ya ce yana daya daga cikin wadanda jami’an tsaro na DSS suka kama suka tsare, na tsawon shekara 4 da wata 3.

Ya ce su bakwai ne da suka hada da shi Kamal Abdullahi da Salim Muhammed da Abdullahi Yahaya da Yasiru Abubakar da Shamsu Idris da Adamu Abdullahi da Ahmed aka tsare na tsawon wannan lokaci.

Ya ce bayan da aka sake su, da aka bi maganar a karshe Gwamnatin Tarayya ta bayar da diyyar Naira miliyan 135 ga Kungiyar Masu Tuka Keke NAPEP ta Garki Abuja domin a biya diyya ga wadanda aka kashe da wadanda aka ji wa ciwo da kuma wadanda aka tsare.

“Bayan  da aka sallami iyalan wadanda aka kashe da wadanda aka ji wa ciwo,  sauran mu da aka tsare sai suka ce sun ware mana namu sun bai wa Shugaban Kungiyar Masu Tuka Keke NAPEP na shiyyar  Garki, mai suna Musa Ibrahim Yalo. Kullum muna zuwa muna tambaya, sai a ce mana mu je gobe mu dawo har yau babu labari,” inji shi.

Ya yi kira ga gwamnati ta taimaka a karbo musu hakkinsu domin har yanzu suna cikin wahala. Kuma a lokacin da aka kama su sun rasa kayayyakinsu, baya ga tsarewar da aka yi musu na tsawon shekara 4 da wata 3.

Wakilinmu ya tuntubi Shugaban Kungiyar Keke NAPEP  na Garki Abuja Musa Ibrahim Yalo kan wannan al’amari, inda ya ce kokacin da kotu ta yanke hukunci kan wannan al’amari a shekarar 2014, ta yanke hukumci ne kan a bai wa wadanda suka rasu mutum 8, Naira miliyan 10 kowannensu da kuma wadanda suka ji rauni mutum 11, Naira miliyan 5 kowannensu.

“Su ne aka biya kuma ni ba a ba ni  kudin kowa ba. Iyalan wadanda suka rasu da wadanda suka ji rauni ne kowannensu ya tura lambar asusun bankinsa kai-tsaye gwamnati ta tura musu wadannan kudi,” inji shi.

Ya ce hukuncin da kotun ta yi ba ta yi magana a biya diyya ga wadanda aka tsare ba. Kuma Naira miliyan 135 aka bayar.