✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a kara samun rushewar wani bene ba – Gwamnatin Legas

Gwamanatin Jihar Legas ta musanta jita-jitar da ake yadawa a kafafen sadarwar zamani da wasu kafafan watsa labarai cewa an samu karin rushewar wani bene…

Gwamanatin Jihar Legas ta musanta jita-jitar da ake yadawa a kafafen sadarwar zamani da wasu kafafan watsa labarai cewa an samu karin rushewar wani bene mai hawa hudu a garin Legas a yammacin ranar Litinin din da ta gabata.

Da yake yi wa manema labarai karin haske bayan yaduwar jita-jitar babban jami’in Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (NEMA), Mista Adesina Tiamiyu, ya ce, ginin mai lamba 57 da ke Unguwar Oke Arin a birnin Legas na cikin gidaje 180 da gwamnatin jihar ta kudiri niyyar rushe su, “Jami’an Hukumar Kula da Gine-Gine ta Jihar Legas (LASBCA) ce ta rushe gidan kasancewarsa daya daga cikin gidajen da suke da hadari, ana kan aikin rushe shi ne buraguzansa  suka rufta wa wadansu mutane masu kalen karafa,” inji shi.

Haka Babban Jami’in Hukumar Kula da Gine-Gine ta Jihar, Injiniya Lekan Shodeinde ya ce, gidan da ake yada jita-jita a kansa mai bene uku hukumar na aikin rushe shi lokacin da ya rufta da masu kalen karafa, don haka ya yi kira ga mutanen da ke zaune a gidajen da hukumar ta ayyana za ta rushe wadanda aka  ba su umarnin barin gidajen su fice su bai wa gwamnatin jihar hadin kai a kokarinta na magance matsalar. Kuma ya gargadi jama’a su rika yin nesa da gidajen da ake aikin rushe su a jihar. Ya ce hukumar kula da gine-gine ce kadai ke da alhakin tantance gidajen da ke cikin yanayin barazana da ya kamata a rushe su ko akasin haka.

Bayan rushewar ginin nan mai bene uku da ya rutsa da yara ’yan makaranta sama da 100 a birnin Legas, gwamnatin jihar ta kudiri aniyar rushe gidaje 180 mafi yawancinsu masu bene uku zuwa hudu, lamarin da a yanzu ya jefa masu haya a gidajen cikin zullumi lura da yadda muhalli ke da wuyar samu a yankin. Ana dai samun  ’yan kadan daga gidajen hayar da dan karen tsada lamarin da ke sanya mutanen kin barin gidajen da aka yi musu alamun za a rushe su. Da yawa daga cikin mutanen da ke haya a irin wadannan gidajen kan gwammace su ci gaba da zama a cikinsu maimakon tunkarar matsalar neman wasu gidajen haya, sakamakom cinkoson jama’a a birnin Legas.