✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a taba cin Masarautar Akko da yaki ba – Sarkin Akko

Mai Martaba Sarkin Akko, Alhaji Umar Muhammad Atiku, Sarkin Yanka ne mai daraja ta daya. A zantawarsa da Aminiya a fadarsa da ke garin Kumo,…

Mai Martaba Sarkin Akko, Alhaji Umar Muhammad Atiku, Sarkin Yanka ne mai daraja ta daya. A zantawarsa da Aminiya a fadarsa da ke garin Kumo, hedikwatar karamar Hukumar Akko, ya bayyana takaitaccen tarihin kafuwar wannan masarauta, inda ya ce ta kafu ne tun a shekarar 1804 lokacin da Amada Gona da Bubayero suka yi karatu tare a wajen Shehu Usmanu danfodiyo suka karbo Tutar Gombe tare. Ga yadda cikakkiyar hirar ta kasance:

 

Aminiya, Ranka dade za mu so jin takaitaccen tarihin kafuwar Masarautar Akko da kuma yawan sarakunan da aka yi?

Gaskiya ba za a iya fadin yawansu ba, amma dai Masarautar Akko ta kafu ne tun a shekarar 1804 kuma lokaci daya aka kafa ta da duk wata Masarauta ta Fulani dake Arewacin Najeriya, domin wadanda suka kafa masarautar fulani ne da suka zo shekaru masu yawa da suka wuce, kuma sun zo ne daga kasar Mali da Senegal a lokacin tun su na shugabancinsu su ya su ana kiransu Ardabai wato Ardo-Ardo, har suka kai ga kame kasashe ta hanyar yakar su a lokacin Usman danfodiyo a shekarar 1804, a wancan lokacin wanda yake shugabantar bangaren fulani namu ne na nan Gona, ana kiransa Amada Gona tare da Bubayero suka je suka yi karatu wanda ya karbo wa Gombe tuta bayan da aka yi yaki aka kafa Daular Usmaniya a Masarautar Gombe a karkashin Modibbo Bubayero, to shi Amada Gona tare suka tafi da Bubayero wajen Shehu Usmanu danfodiyo kuma kamar yadda tarihi ya nuna cewa shi ma Amada Gona, Shehu ya yi masa tayin tuta kamar yadda ya bai wa Bubayero, amma sai ya ce a’a, wanda aka bai wa Bubayero ta ishe su dukansu biyun. 

Bayan sun dawo Amada Gona su ne fulanin wannan kasar Bubayero kuma fulanin kasar Sheleng ne a Fetambere da Bubayero ya wuce kasar su bai samu karbuwa a wajen ‘yan uwansa ba, sai ya dawo nan ya sake haduwa da shi Amada Gona da sauran Fulanin da suke nan aka yi yaki aka kafa daula, da yake lokacin ya samu dattawa ne sai suka ce shi Bubayero din ya shugabance su a matsayin Sarki na farko a Daular Usmaniya a Masarautar Gombe, ana tafe da wannan tarihi har shekara ta 2001 lokacin da aka fasa Masarautar Gombe aka kirkiro da karin Masarautu guda bakwai da suka hada da Masarautar Akko kanta da Dukku da Deba da Yamaltu, a lokacin akwai Jara wanda yanzu babu ita an rushe ta, akwai Nafada da Funakaye, daga baya a shekara ta 2007 aka yi canje-canje wajen daga darajojinsu daga masu daraja ta biyu zuwa masu daraja ta daya, har ila yau ana tafe har aka sake kirkiro da wasu masarautu kuma daga jikin Masarautar ta Akko aka cire Gona ta fita daga Akko, aka cire Pindiga hakan kuma ya biyo bayan yawan jama’a ne da suke karuwa.

Daga dai lokacin da aka kirkiro da Masarautar Akko zuwa yanzu, an yi manyan sarakuna guda biyu, na farko ya fara daga shekara ta 2001 zuwa 2004, wanda a lokacin ne ni na karbe shi har zuwa yanzu. A karamin tarihi daga 1804 zuwa yanzu Sarakunan da aka yi za su kai 18 wadanda a wancan lokacin suna matsayin Galadima ne, wato Hakimai ne da suke karkashin Masarautar Gombe har zuwa 2000, abun da ya biyo baya daga shekarar 1804 nan ma akwai jerin shugabanni na wannan masarauta ta Akko da suke karkashin Fulanin Gona suma za su kai fiye da 10, idan aka hada duka a wannan masarautar an yi sarakuna da ba za su gaza 30 zuwa 40 ba.

Aminiya: An taba cin Akko da yaki a tarihi ko kuwa?

A’a, lailai babu batun an ci Akko da yaki, wannan bai zo a tarihinmu ba sai dai wuraren da suka zamo a karkashin wannan masarauta, domin lokacin da Akko take Akkonta, iyakokinta idan ka yi gabas tana iyaka da Masarautar Waja, a Arewa kuma ta na iyaka da Dukku, domin ta wuce Gombe! Inda Gombe take a yanzu Akko ce  ta bai wa Sarkin Gombe dan a yi helkwatar Gombe a wajen. Ta yamma kuma Akko ta kai har kusa da Dindima na kasar Bauchi, sannan irin su Deba da Dadin-kowa duka suna karkashin Masarautar Akko ne, haka Pindiga ma tana karkashin Akko. A wancan lokacin babu batun Tangale a lokacin duka suna karkashin Akko ne, ba za dai a rasa ‘yan hare-hare ba, amma babu wadanda suka yi tasiri a cikinsu dan ko yake-yake da aka yi lokacin zuwan turawa, ita Akko ba ta tabu ba sosai, akwai wani yaki da aka kawo daga Nbormi wani mutum daga garin Misau suka zo suka kawo hari a Akko lokacin hedikwata tana can Akko, kuma akwai mazauni mai karfi a garin Tukulma wadanda duka na Fulanin Gona ne, wadannan runduna ta zo aka samu hadin baki da Masarautar Gombe akan sai aje a yaki Akko, amma an yi watanni ana kewaye da Tukulma, amma haka aka hakura ba a samu nasara ba. Wadanda suka kawo harin haka suka koma inda suka fito, daga nan sai aka samu cigaba da zaman lafiya a lokacin da take da karfin ta babu wanda ya isa ma ya tunkare ta da yaki, dan Masarautar Gombe ma a lokacin Galadiman Akko shi yake nada Sarki, kuma idan aka nada wanda bai masa ba yana iya sauke shi yasa wanda yake so, tun da tarihi ya nuna an taba yin hakan saboda Allah Ya azurta su da jarumai horarru a bangaren yaki ga dawakai da kuma sanin yadda ake sarrafa karfe.

Aminiya: Ko akwai wasu bukukuwan tarihi na al’ada a Masarautar Akko baya ga hawa dawakai?

Kasancewar musulunci ya jima a Masarautar Akko, hakan ya sa an jima da kawar da duk wasu wasanni na al’ada wanda musulunci bai koyar da su ba, ba mu da wani wasan al’ada da ya wuce wasan hawan dawakai a bukukuwan Sallah, kamar hawan Daushe sai kuma bukukuwan Aure bayan su ba mu da wasu bukukuwa da muka bari ya shige mana ido wanda ya sabawa addini.