✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a yi wa Musulmin Kudancin Kaduna adalci kan rikicin zaben 2011 ba –  SOKAMUDA

Al’ummar Musulmin Kudancin Kaduna wadanda rikicin siyasar 2011 ya rutsa da su sun ce har yanzu ba a yi musu komai na adalci ba. Da…

Al’ummar Musulmin Kudancin Kaduna wadanda rikicin siyasar 2011 ya rutsa da su sun ce har yanzu ba a yi musu komai na adalci ba.

Da yake jawabi a wajen taron tunawa da wadanda aka kashe a lokacin rikicin kusan shekara takwas da suka gabata da aka shirya a Kaduna, Shugaban Kungiyar Al’ummar Musulmin Kudancin Kaduna (SOKAMUDA), Alhaji Adamu Muhammad Kagarko ya ce har yanzu marayun da aka bari na fama da wahala.

Ya bayyana cewa akalla mutane sama da dubu daya aka kashe sannan iyalai sama da dubu 25 aka tarwatsa daga gidajensu a garuruwan Zonkwa da Matsirga da Kafanchan da Gidan Maga da Kagarko da Madakiya da Kwoi da sauransu.

“A cikin kwana biyu mun rasa mutum akalla 1000 da gonaki da gidajenmu a wadannan garuruwa na Kudancin Kaduna. Kuma abin bakin ciki shi ne har yanzu akasarin wadanda suka aikata wadannan laifuffuka ba a kama su ba. Har yanzu al’ummarmu ba su samu adalci ba, don haka muka taru a nan domin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu tare da yi musu addu’ar Allah Ya jikansu. Muna kuma son mu tuna wa gwamnati cewa marayu da mata da aka kashe wa iyaye da mazaje na cikin mawuyacin hali da ya kamata a kai musu dauki,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa “Mafi yawancinsu suna zaune a gidajen haya ne a garin Kaduna da kewaye domin sun kasa komawa gidajensu na asali tun wancan rikici. Baya ga haka kuma muna sanar da gwamnati cewa diyyar Naira biliyan bakwai da aka yi wa wadanda suka yi hasara alkawari Naira biliyan uku kawai aka bayar yanzu saura biliyan hudu ba a bayar ba.”

A jawabin Alhaji Abdullahi Hassan Muhammad wanda basarake ne a Masarautar Jama’a ya ce har yanzu ba su mance da wadanda aka kashe a lokacin rikicin ba.

Sai dai ya shawarci gwamnati  ta kai wa wadanda abin ya shafa dauki musamman marayu da mata domin su samu saukin rayuwa.

Ya ce za a ci gaba da tunawa da wadanda aka kashe duk shekara domin tuna irin ta’asar da aka aikata ga al’ummar Musulmin yankin.

Wadansu daga cikin wadanda rikicin ya rutsa da su sun nuna takaicinsu kan irin halin ko-in- kula da Gwamnatin Tarayya ke nuna musu duk da cewa su ma ’yan Najeriya ne kamar kowa.

Sani Zonkwa daya daga cikin ’yan gudun hijirar ya ce, “Gaskiya halin da muke ciki shekara takwas bayan rikicin babu dadi domin har yanzu babu wani abu da gwamnati ta yi mana. Mu ’yan Najeriya ne kuma ’yan Jihar Kaduna da aka haifa a Kudancin Kaduna, amma kullum da an tashi magana sai a ce Maiduguri, mu kuma muna ganin duk wani tashin hankali da ’yan Maiduguri suka gani mu ma mun gani.”

Shi ma Awwal Idris Matsirga ya ce yanzu duk jama’ar Matsirga sun watse suna haya a garuruwa irin su Rigasa da Kafanchan da Rigachikun da Gidan Abe da Sabon Wuse a Neja.

Ya ce gidajensu da gonakinsu duk sun zama na wadanda suka kashe su ko suka kore su daga garin Matsirga shekara takwas da suka wuce kuma ba su iya komawa can garin. Don haka sai ya nemi gwamnati ta taimaka a karbo musu dukiyoyinsu sannan a mai do da zaman lafiya a yankin Kudancin Kaduna.