✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba a bi hanyoyin da suka dace wajen kafa sabbin masarautun Kano ba- Shaikh Daurawa

Shahararren malamin nan na Kano Shaikh Amin Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano bata bi hanyoyin da suka dace ba wajen kafa sabbin…

Shahararren malamin nan na Kano Shaikh Amin Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kano bata bi hanyoyin da suka dace ba wajen kafa sabbin masarautu hudu a jihar, ya ce kamata ya yi gwamnatin ta gudanar da kuri’un jin ra’ayin jama’ar jihar Kano kafin ta kai ga kirkirar masarautu. “Kamar yadda wadanda suka kirkiri masarautun suke fada sun yi haka ne domin bunkasa tattalin arzikin jihar da kuma ci gaban al’ummarta, idan haka ne wannan manufa ce mai kyau, amma ba a bin hanyoyin da suka dace ba wajan kirkirar masarautun.” In ji shi.

Ya ce, kirkirar karin masarautun a Kano lamari ne da zai haifar da gaba da rarrabuwar kai a tsakanin jama’ar jihar tare da zubar da daraja da kimar masarautun gargajiyar jihar.

Ya ce,  sama da shekara dubu ke nan Mujadaddi Shehu Usmanu Danfodiyo, ya yi kokarin kafa masarautar Kano inda ake da Sarki guda wanda ya hade kan al’ummar jihar dan haka ba daidai bane a lokaci guda wani yazo ya rushe wannan dadadden tarihi domin musgunawa wani ko faranta wa wasu ba, ya ce a ra’ayin su na malamai shi ne ayi abin da zai kawo wa jihar Kano ci gaba da hadin kan al’ummar ta duk wani abu da zai zamo akasin haka ya jawo gaba da rarrabuwar kan al’umma basa tare da shi.

Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana haka ne a ganawarsa da manema labarai a sa’ilin rangadin da ya yi a garin Agege a Legas, inda ya gabatar da karatun wa’azi na maza a daren Larabar da ta gaba ta yayin da ya gabatar da wa’azin mata da safiyar Alhamis.

Manyan malaman addinin musulunci na ci gaba da tsokaci bisa sabbin masarautun da gwamnatin jihar Kano ta kirkiro inda a jiya Alhamis gwamnan Kano Dakta Abudullahi Umar, ya sanyawa dokar ƙirƙirar sabbin masarautun hannu bayan da wata kotu a Kano ta soke su, sabbin masarautun da suka hada na Bichi da Karaye, sai Rano da Gaya.