✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba adalci sukar ’yan majalisar da suka yi ihu ga Buhari

Assalam Edita. Masu sukar ’yan majalisar da suka yi wa Shugaba Buhari ihu lokacin da yake gabatar da kasafin kudin badi a zauren Majalisar Wakilai.…

Assalam Edita. Masu sukar ’yan majalisar da suka yi wa Shugaba Buhari ihu lokacin da yake gabatar da kasafin kudin badi a zauren Majalisar Wakilai. Hakan da kuka yi ba adalci ba ne.Ya kamata ku ajiye adawa ko makauniyar soyayyar da kuke yi wa Buhari ku yi adalci ta hanyar fara sukar ’yan majalisar da suka fara cewa, sai Baba! Sai Baba! Lokacin da Buharin ya zura kafarsa a cikin zauren majalisar. Zauren majalisa ba wurin yi wa wani yakin neman zabe ba ne. Domin wadanda suka yi ihun su ma suna da nasu gwanin amma ba su kira sunansa sun tallata shi a zauren ba! Saboda haka in anbi ta barawo a bi ta ma bi sawu. Dukansu sun aikata laifi saboda haka bai kamata a danne laifin wadansu a nuna na wadansu ba. Da fatan za mu rika yi wa kowa adalci.

Daga Haruna Muhammad Katsina, Shugaban Kungiyar Muryar Jama’a. 07039205659.