✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba alamar Coronavirus ga wadanda ake zargi a Kafanchan – Dakta Habila

An tabbatar da wadanda ake zargi da harbuwa da cutar coronavirus a garin Kafanchan a jihar Kaduna da cewa babu wata alama na cewa suna…

An tabbatar da wadanda ake zargi da harbuwa da cutar coronavirus a garin Kafanchan a jihar Kaduna da cewa babu wata alama na cewa suna dauke da cutar, duk da cewa an debi samfurin da za a kai Legas don aunawa.

Shugaban tawagar jami’an kiwon lafiya kuma mamba a tawagar kai dauki ga masu cutar Covid-19 a jihar Kaduna, Dakta Kambai Habila ne ya bayyana hakan jim kadan bayan sun auna tare da daukar samfur daga ‘yan mata biyun da aka killace su a asibitin Kafanchan bisa zargin bayyanar alamomin cutar.

Ya ce za a tafi da samfurin jihar Legas tare da sauraron sakamako na karshe a ranar Laraba.

“Kama daga tambayoyi zuwa ‘yan gwaje-gwajen da muka gudanar yanzu, babu alamar cutar coronavirus a tartare da su, amma ganin yadda hankalin jama’a ya tashi ne yasa muka debi samfurin da ake diba kuma zuwa ranar Laraba za a ji sakamakon karshe na gwajin.” In ji shi.

Shi ma shugaban karamar hukumar Jama’a, Danjuma Peter Averik wanda ya kasance da tawagarsa a asibitin har zuwa kammala daukar samfurin, ya jawo hankalin jama’a da su zamo masu kula da kansu sannan su guji yada jita-jita kan wannan cuta.

Averik, ya ce kofar su a bude take a duk lokacin da aka ji wani kishin-kishin na alamomin cutar a jikin wani domin daukar matakin na gaggawa don tantancewa, maimakon yada jita-jita da sanya fargaba a cikin jama’a ga abin da ba a tabbatar da shi ba tukunna.

Su dai wadannan ‘yan mata an ce daya daga ciki ta dawo ne daga jihar Lagos, jihar da tafi ko ina a fadin Najeriya dauke da masu cutar, abin da ya janyo karin fargaba ga makwabta da jama’ar unguwar da matan suke a unguwar Mishan da ke Garaje a bayan garin Kafanchan.