✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba almajiranci ne matsalar tsaro a Najeriya ba – Sheikh Jingir

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir shi ne Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa. A tattauna da wakilinmu, kan…

Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir shi ne Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa. A tattauna da wakilinmu, kan yunkurin Gwamnatin Tarayya na hana almajiranci a Najeriya, ya ce ba almajiranci ne matsalar tsaro a Najeriya ba:

Gwamnatin Tarayya tana yunkurin hana almajiranci a Najeriya bisa abin da ta kira yunkurin magance matsalar tsaro, Me Malam zai ce game da wannan yunkuri?

To gaskiya wannan magana ta hana almajiranci don inganta tsaro a Najeriya, magana ce wadda ta kunshi wani dunkulallen abu da yake bukatar a yi bayani. Domin idan ka ce da ni matsalolin tsaro da yadda suka shafi al’umma a Najeriya, sai in ce maka kututun rashin tsaro a Najeriya shi ne gidajen karuwai da suke tara barayi da ’yan fashi. Haka da gidajen shaye-shayen giya da miyagun kwayoyi da gidajen tsafi da ake kama yaran mutane, ana kaiwa ana yin tsafi da su. Har ila yau da dibar ’yan sanda wadanda su ne suka fi kowa kusa da jama’a, marasa karatu da tsoron Allah, wadanda ake hada baki da su, su gaya wa barayin wajen da za su fita da lokacin da za su fita. Haka da ma’aikatan da suke rike da madafun mulki da suke karbar cin hanci da rashawa a kasar nan. Da gidajen rediyo da talabijin da jaridu da mujallu da ake koyar da fitsara da fashi da makami da bata tarbiyya.

Wadannan wurare duk wanda ya ce zai yi tsarin tsaro ya yi biris da su, ya je yana kame-kame bai yi nufin gaskiya ba. Kuma idan muka dawo kan maganar almajirai da almajiranci, idan muka dauki almajirai a nan kasar Hausa, wato kamar mutum ne ya sa rai gwamnatin karamar hukuma ko jiha ko tarayya, idan aka zo rabon dukiyar kasa za a karfafi ilimi a raba kudin kowa ya samu nasa.

Sai ya ga gwamnatin ta yi wariya ta dauki bangaren ilimin boko ta ce shi ne ilimi, ta zubar da ilimin addinin Musulunci. Amma kuma za ta iya karbar haraji a wajen mai ilimin addinin Musulunci amma babu ruwanta da ilimin da wannan mai ilimin ya amince da shi sama da shekara 300.

Gwamnatin Shehu Usman Dan Fodiyo da ilimin addinin Musulunci ta gudanar da mulkin kasar nan sama da shekara 200. A lokacin ba a samu ’yan fashi da makami da karuwai da ’yan cin hanci ba. Abin takaici ne idan an zo raba arzikin kasa babu kason almajirai da za a lura da makarantunsu a kananan hukumomi da jihohi da tarayya, gwamnati ta kame hannunta tana son ta ce su iliminsu ba ilimi ba ne, ta mayar da hankali kan ilimin boko kadai.

Alhalin sai mutum ya dauki dansa ya kai makarantar boko da ya karbi satifket din gama firamare da sakandare wani sai ya dawo gida yana shan taba, wani ya dawo yana shan giya, wani ya dawo ba ya da kunya wanda a da duk ba a san shi da irin wadannan miyagun abubuwa ba.

Wannan ne ya sa mutane suka rika kyamar karatun boko da gwamnati take bayar da kudi a kansa. Suna gudu da ’ya’yansu suna neman inda za su je su yi karatun addinin Musulunci, ita kuma gwamnati ta ki ta gyara manhajar wannan bangare.

Saboda haka idan aka lura da almajirai, duk masifun da rashin tsaro ya kawo a Najeriya kansu yake karewa. Ana sace su ana sayarwa, wadansu ana cinye su, domin gwamnati ta yi watsi da tsarin karatunsu. Wanda kuma ilimi ne ake koyarwa, an yi rubuce-rubuce masu tarin yawa kan harkokin gwamnati da bayanai kan zamantakewar jama’a da harkokin shari’a da sauransu da rubutun ajami ta wannan ilimi da suke koyarwa.

Kuma yanzu sai ana cewa wai almajirai sun kawo rashin tsaro a Najeriya. Duk wadanda suka fadi wannan magana ba su yi adalci ba, domin sun yi shiru kan gidajen giya da gidajen karuwai da gidajen tsafi.

To ina mafita kan wannan al’amari?

A gyara tsarin karatun almajiranci, a ba su kasonsu na dukiyar Najeriya, a inganta makarantunsu. Kuma a gyara tsarin karatun boko a Najeriya ya zamo yaron da ya yi makaranta ya karanci koyon sana’a. Ba yaro da zarar ya gama jami’a ya ce ya fi karfin ya yi noma da kiwo ko kasuwanci ba, domin babu gwamnatin da za ta dauki dukkan yaran da suka gama karatun jami’a ta ba su aiki. Wanda ya yi karatu bai san sana’ar da zai yi ba, shi ne matsalar kasa ba almajiri ba. Shi almajiri mara gata ne a wajen gwamnati da Turawa suka yi mata tsarin karantarwa. Saboda haka ni abin da nake gani, almajiran nan suna bin gwamnati bashi  ne kuma ga shi an zo ana cewa wai su ne suke kawo matsalar tsaro a Najeriya.

Yanzu aikin jaridar nan da kuke yi babu wanda ba za mu iya yi da ajami ba amma an ce ba a son namu ilimin, sai wanda Turawa suka kawo, ka ga an danne mana hakki. Kuma da an yarda ana buga mana jaridu da rubutun ajami, an yi litttafan lissafi da na ilimin kimiyya da fasaha da noma da kiwo da miliyoyin masu iya ajamin nan za su amfana.

Sai da na shekara sama da 25 ina wa’azi kan a bude mana gidajen jaridu na Hausa. Sannan muka samu aka bude mana wadannan sababbin gidajen jaridu na Hausa. Sakamakon bude wadannan gidajen jaridu na Hausa yanzu mutanenmu suna karanta abubuwan da suke faruwa.

A karshe wane sako ne Malam ke da shi ga gwamnati game da wannan lamari?

Sakona ga gwamnati shi ne, kamar yadda na fada a baya, ta karfafa tsarin ilimi a kasar nan, ta gyara manhajar koyarwa ta yadda duk wanda zai yi karatun boko ya hada da koyon sana’a. Kuma wanda suk zai yi karatun addinin Musulunci ya hada da koyon sana’a. Domin tsarin manhajar da ake amfani da shi yanzu a Najeriya, ba ya da kyau. A ce har yanzu duk jami’o’in da muke da su a Najeriya babu jami’ar da ta kirkiro yadda za a yi keke, wannan bai dace ba.