✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba da mu sojoji ke fada ba – Tubabun ’yan bindigar Zamfara

Tubabbun ’yan bindiga a Jihar Zamfara sun ce su ba ruwansu da farmakin da sojoji ke kai wa a kan sansanonin barayin shanu a jihar,…

Tubabbun ’yan bindiga a Jihar Zamfara sun ce su ba ruwansu da farmakin da sojoji ke kai wa a kan sansanonin barayin shanu a jihar, inda suka ce wadanda suka ja rikicin da sojojin su rikicin zai ci.

Wadansu daga cikin tubabbun ’yan bindigar da suka zanta da wakilinmu ta tarho sun ce duk da su ma ba su ji dadin abin da ya faru a tsakanin sojoji da barayin shanun ba, to amma ba ruwansu kuma wadanda suka yi fada da sojoji, su lamarin ya shafa.

“Babu abin da ya shafi yarjejeniyarmu da gwamnati da ’yan sa-kai. Hasali ma ba mu san wadancan barayin shanu ba ko kuma mece ce manufarsu kuma inda za ka fahimci haka, ai ba ka ji labarin kai hari a wani gari ba. To amma ba mu ce ba za su iya samun hadin kai daga wasu kangarrarru daga cikinmu ba, kuma ban ce babu su ba amma dai mu shugabanninsu muna sa ido sosai kuma muna sanar da hukumomi abin da duk ke faruwa a dazuzzukan wannan jiha,” inji Ado Ali.

Mai ba Gwamnan Jihar Zamfara Shawara kan Sha’anin Tsaro, Alhaji Abubakar Dauran ya ce wadanda suka yi fada da sojoji ba daga Jihar Zamfara suke ba, kuma fadan ko kadan bai shafi sulhun da aka yi da ’yan bindigar ba.

“Kada ka manta, jihohi kamar Sakkwato, Kebbi, Kaduna, Neja da Katsina duk suna da irin wadannan barayin shanu kuma wadannan mutane, ga rahoton da muka samu sun ketaro ne daga wadancan makwabtan jihohi, don su saci shanun jama’a kuma sojoji sun kwace shanun da suka sata a Karamar Hukumar Bukuyyum,” inji shi.

“Akwai shanu sama da dubu da sojoijin suka kwace a hannun barayin kuma sun dauki matakin ne don hana barayin tserewa da shanun sata wadanda galibinsu an sato su ne daga makwabtan jihohi. Su kansu wadansu daga cikin mutanen wannan jihar, an sace masu shanu kuma ana tantance masu shanun domin mai da masu. Mun kira taron gaggawa da  shugabbanin tubabbun ’yan bindigar kuma sun shaida mana cewa babu ruwansu da abin da ke faruwa kuma za su ba gwamnati goyon baya domin bankado masu hannu a ta’asar da wadansu ke tafkawa a dazuzzukan jihar,” inji shi.

A makon jiya ne sojojin suka kai samame a sansanonin ’yan bindigar da ke dajin Sunke da Bawar Daji a Karamar Hukumar Anka, kuma sojojin sun yi nasarar hallaka ’yan bindiga 59  tare da kwace alburusai da bindigogi da dama.

Harin da sojin suka kai ya zo mako daya bayan da ’yan bindigar suka kai wa sansanin sojojin hari suka kashe tara daga cikinsu. Masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin harin sojan kan ’yan bindigar wata ramuwar gayya ce ta jami’ansu da aka kashe.