✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba daidai ne malamai su ce a zabi wane ba – Farfesa Makari

Daya daga cikin manyan limaman Masallacin Kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Ahmad Makari ya ce ba daidai ba ne malaman addini su kama sunan…

Daya daga cikin manyan limaman Masallacin Kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Ahmad Makari ya ce ba daidai ba ne malaman addini su kama sunan wani dan takara su ce jama’a su zabe shi.

Farfesa Ibrahim Makari ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da Aminiya bayan da wasu kungiyoyi da daidaikun mutane suka fara fitowa fili suna bayyana sunayen ’yan takarar da za su marawa baya. Farfesa Makari ya bayyana wa Aminiya haka ne a lokacin taron Maulidin da kungiyar Abuna’ul Faidah ta shirya a Legas a karshen makon jiya. Ya ce yin hakan ya saba wa ka’idar addinin Musulunci, “A wannan lokaci na zabe lokaci ne da malamai ke dukufa wajen yi wa kasa addu’a kuma su wayar wa al’ummarsu kai kan muhinmmancin kuri’arsu domin ita kuri’a amana ce kuma Allah Zai tambayi mutum yadda ya yi amfani da ita, don haka kada su sayar da kuri’unsu don neman dan abin duniya. Kada su yi amfani da ita bisa son zuciya, ba daidai ba ne shugabanin addini su fada wa mabiyansu ku zabi wane ko kada ku zabi wane, wannan ba koyarwar addini ba ce, abin da muka ga magabata sun yi a kan wannan shi ne bayanna wa mabiyansu kyawawan sifoffin shugaba nagari, nagartaccen shugaba shi ne mai gaskiya da rikon amana,” inji shi.

“Sannan masani a harkokin jagoranci da mulkin al’umma tare da jan ragamarsu, wannan su ne sifoffin da ya kamata a nusar da mabiya, idan sun zo kada kuri’arsu amma ba daidai ba ne ka kama sunan wane ka ce wa mabiyanka su zabe shi, yin haka ya saba wa tsarin koyo da koyarwa,” inji shi.

Mauludin wanda ya samu halartar manyan malamai daga ciki da wajen kasar nan ciki har da Limamin Ghana, Dokta Usman Nuhu Sharubutu da Farfesa Abubakar Yagawal, inda suka shirya addu’o’i na musanmman ga kasar nan da al’umma lura da karatowar lokacin zabe mai zuwa.