✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba domin siyasa nake tallafa wa jama’a ba – Tsauri

Wani dan siyasa a Jihar Katsina Alhaji Umar Abdullahi Tsauri da ake wa lakabi da Tata, ya ce ba siyasa ta sanya shi aiwatar da…

Wani dan siyasa a Jihar Katsina Alhaji Umar Abdullahi Tsauri da ake wa lakabi da Tata, ya ce ba siyasa ta sanya shi aiwatar da ayyukan tallafa wa jama’ar jihar ba.
Alhaji Umar Tsauri ya bayyana haka ne a jawabinsa wurin tantance matan da za su gajiyar tallafin kayayyakin koyon sana’a da aka raba wa matan da mazajensu suka rasu da kuma marayu dubu uku a yankin Funtuwa a ranar Asabar da ta gabata.
Ya ce in ma an dauka siyasa ce, tasa yake wannan aiki, to duk matar da ta samu wannan tallafi, ba ya bin ta bashi, ballantana ta yi tunanin idan ranar zabe ta zo, lallai sai ta zabe shi.
“Ni tamkar dan sako ne ko gidan waya, don haka wadda ta samu kasonta a cikin wannan tallafi, Allah ne Ya kaddaro rabonta ya biyo ta hannuna. Kuma ba siyasa ba ce ta sanya ni wannan aiki. Idan har siyasa nake yi, to akwai wadanda suka fi ni a wurin nan, mutane irin su Alhaji Garba Aminci su ne kurungus a siyasa. Ba na bin kowace mace bashi, idan har Allah Ya kaddara na samu takara, to a ranar zabe idan har an ga rashin cancantata kada a zabe ni,” inji shi.
A jawabin tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Abdulahi Garba Aminchi wanda tsohon Jakadan Najeriya ne a Saudiyya, ya bukaci ’yan siyasa su yi koyi da wannan kokari na Alhaji Umar Abdullahi Tsauri.
Shugaban kungiyar Izala na Jihar Katsina, Sheikh Yakubu Musa Hassan, ya bayyana yadda kungiyar ke karbo tallafi daga mawadata tana raba wa masu rauni a cikin al’umma, wadanda suka hada da matan da mazansu suka rasu da zawara da marayu. Don haka sai ya bukaci ’yan siyasa su yi koyi da Tata. “Mu ba ruwanmu da bambancin siyasa, matukar mutum zai taimaka wa marayu, to muna da kwamitin marayu na kasa, wanda ke karkashin jagorancin Alhaji Abdullahi Garba Aminci. Don haka a shirye muke mu taimaka wa duk wanda zai gudanar da irin wannan aikin alheri,” inji shi.
Raba tallafin wanda ya gudana da hadin gwiwar kungiyar Izala a garin Funtuwa, manyan malaman kungiyar sun gabatar da wa’azin kan muhimmancin taimakon marayu da irin ladar da Allah ya yi tanadi kan irin wannan gagarumin aiki.
Daga cikin malaman da suka yi wa’azin akwai Sheikh Haruna Kabiru Gombe, wanda ya bayyana gwaggwabar ladar da ke ga duk mai taimakon maraya. Sannan ya yi tsokacin kan yadda kungiyarsu ke yunkurin shirya aurar da zawarawa da gwagware.
Shugaban kwamitin raba kayan tallafin, Alhaji Tijjani Muhammad Bakori, ya cewa an raba kayan da suka hada da motoci kirar Fijo 806 guda 10 da babur mai kafa uku 20 da baburan hawa 1,020 da kekunan dinki 1,200 da injunan nika da na saka 2,217 da kudinsu ya kai Naira miliyan 95.
Alhaji Tata ya alkawarta wa kungiyar Izala daukar dawainiyar aurar da zawarawa da gwagware da ta ce za ta yi. “Idan har mutum ya samu mace, kuma ya gaza daukar dawainiyar auren to sai a biyo ta hannun Malam Yakubu Musa Hassan, in Allah Ya yarda za mu yi wannan aure,” inji shi.