✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba Fulani ne kadai ke aikata miyagun ayyuka a kasar nan ba – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’adu Abubakar, ya ce babban kuskure ne a dora wa al’ummar Fulani su kadai laifin aukuwar miyagun ayyuka a…

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’adu Abubakar, ya ce babban kuskure ne a dora wa al’ummar Fulani su kadai laifin aukuwar miyagun ayyuka a kasar nan. Kuma ya ce idan mahukunta ba su hanzarta daukar mataki don shawo kan yadda ake jingina wa Fulani duk wata barna ba, to yana iya haifar da gabar kabilanci a tsakanin kabilun kasar nan.

Sarkin Musulmi ya fadi haka ne a jawabinsa a wajen bikin bude sabon Masallacin Juma’a na Sheikh Idrees Faazazi Mogaji a garin Iwo a Jihar Osun a ranar Asabar da ta gabata. Babban Sakataren Kungiyar Muslim Ummah (MUSWEN) a Kudu maso Yamma Farfesa Dawud Noibi ne ya wakilci Sarkin Musulmi a wajen bikin bude babban masallacin da Sheikh Idrees Faazazi wanda ake yi masa lakani da Iwon Malamai ya gina.

Sarkin Musumi,  ya ce da yawa daga cikin miyagun ayyuka da ake yi a wannan sashe ana yin su ne tare da mutanen yankin. “Dukkanmu muna sane cewa wadansu mutane a kasar Yarbawa suna hada kai da masu satar mutane da aikata wasu miyagun ayyuka wadanda babu inda suka sani a wadannan wuraren sai da hadin bakin ’yan gari suke aikata danyen aikinsu.  Ana ba su matsuguni a boye da ciyar da su abinci,” inji Sarkin Musulmin. Ya ce, gyaran dukkan irin wadannan abubuwan yana rataye ne a wuyan dukkanmu ’yan Najeriya.

Ya  roki limamai da malaman addinin Musulunci a kasa baki daya su yi amfani da masallatai da makarantu wajen yawaita tunatar da al’ummarsu domin ganin sun canja halayensu na miyagun ayyuka saboda bayan mutuwa, kowa daga cikinmu zai yi bayanin irin abubuwan da ya aikata a gaban Allah.

Mai masaukin baki Oluwo na Iwo Oba Abdulrasheed Akanbi, shi ne ya yanke kyallen bude masallacin a gaban manyan sarakunan Yarbawa da manyan malamai da dubban Musulmi maza da mata na ciki da wajen garin.