✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba gudu, ba ja da baya a kan zaftare alawus din ’yan kwallon Super Eagles -Hukumar NFF

A ranar Juma’a da ta wuce ne Hukumar kwallon kafa ta Najeriya da aka fi sani da NFF ta fitar da sanarwar cewa babu gudu…

A ranar Juma’a da ta wuce ne Hukumar kwallon kafa ta Najeriya da aka fi sani da NFF ta fitar da sanarwar cewa babu gudu kuma babu ja da baya a hukuncin da ta yanke na zaftare alawus din ’yan kwallon kafa na Super Eagles daga Dala dubu goma kwatankwacin Naira miliyan daya da dubu 600 a kan duk wasan da suka samu nasara zuwa Dala dubu 5 kwataniwacin Naira dubu 800.
Hukumar ta bayyana haka ne jim kadan bayan ’yan wasan sun gudanar da zanga-zangar lumana a Amurka kafin a shawo kan al’amarin daga nan suka zarce zuwa kasar Brazil don halartar gasar cin kofin zakarun Nahiyoyi (Confederations Cup).
A kwanakin baya ne dai Hukumar ta ce ta yanke shawarar ba ’yan wasan alawus din Dala dubu 5 ne ga duk wasan da suka samu nasara da kuma Dala dubu 2 da 500 a wasannin da suka yi kunnen doki.
Sakatare Janar na Hukumar NFF Musa Amadu a lokacin da yake karin haske ga manema labarai a Abuja, ya ce batun da Abba Yola, Shugaban kulob din Kano Pillars ya yi cewa bai ga dalilin da zai sa hukumar ta zaftare alawus din ’yan kwallon a wannan lokaci ba tun da ya zama al’ada zancen ba haka ba ne.
Sakataren ya ce ganin yadda Hukumar ta fada tarkon matsalar tattalin arziki a wannan lokaci babu yadda za a yi hukumar ta cigaba da biyan ’yan wasan alawus din Dala dubu 10 don haka ba ta dauki wannan mataki don kuntata wa ’yan kwallon ba ne kuma akwai yiwuwar nan gaba idan al’amurra suna daidaita a koma ’yar gidan jiya.
“Mun yi mamakin ganin yadda Abba Yola ya shiga kakafen watsa labarai yana bayani akan cewa tuni Hukumar ta zartar da hukuncin biyan ’yan wasan Super Eagles alawus din Dala dubu 10”, inji Musa Amadu.
“Babu wata yarjejeniya da muka yi a rubuce a kan haka, don haka Hukumar tana amfani da zahiri ne wajen biyan ’yan kwallon, yanzu da al’amurra suka tabarbare tilas mu canza taku”, inji shi.
Al’amarin zaftare alawus din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ya janyo cece-ku-ce a tsakanin Hukumar da ’yan wasan kuma da kyar da jibin goshi wasu masu fada a gwamnati suka lallashe su zuwa gasar zakarun Nahiyoyi da ke gudana a Brazil a lokacin da kungiyar ke atisaye a Amurka.
Sai dai da yawa daga cikin ’yan kwallon sun nuna har yanzu ba ta sake zane ba don akwai rina a kaba gane batun zaftare musu alawus da hukumar ta yi.  Kenan akwai yiwuwar su yi wa hukumar tawaye a nan gaba.