Da Dumi Dumi

‘Ba ma maraba da Gwamna Matawalle a APC’

Kungiyar Matasa masu kishin jihar Zamfara ta ce ba ta maraba da Gwamnan Jihar Zamfara, Gwamna Matawalle na Jam’iyyar PDP.

Aminiya ta ruwaito a tattaunawarta da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Sani Ahmed Yariman Bakura, inda ya ce ’yan siyasar Zamfara kansu a hade yake, inda ya ce suna tattaunawa a tsakaninsu, kuma suna sa ran za su sake hadewa nan gaba.

Sakataren kungiyar, Alhaji Musa Gusau ya ce “Hakika wannan ba abin mamaki ba ne idan aka ce wannan bayani ya fito ne daga bakin tsohon gwamna domin kowa ya san irin sabon salon siyasa “Me fuska biyu” da  ya dauko.

“Duk bayan zargin Yarima da zama silar dukkan wasu matsaloli da jam’iyar APC ta fuskanta a zaben shekarar 2019 da ya gabata, tare da goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar G-8 don tarwatsa jam’iyar APC a Zamfara a bangare daya wanda aka yi nasara a wancan  karon.

“Yanzu  kuma sai ga   wannan yunkuri nasa na dawowa da Gwamna Bello Matawalle zuwa jam’iyar APC, saboda wani boyayyen kuduri nasa, da kuma shirye-shiryensa na takarar kujerar Shugaban Kasa a zaben 2023 mai zuwa da kudaden zamfarawa.

ADVERTISEMENT

“Ba ma ganin akwai wani yunkuri da zai hana tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari  zama Shugaban jam’iyar APC na kasa, bayan dukkansu sun fahimci tabbaci da bayanai na cewar dukkan masu fada aji a jam’iyar APC dama dattawan Najeriya sun ba da goyon baya wajen tabbatar da tsohon Gwamna  a matsayin sabon Shugaban Jam’iyar APC na Kasa don samun nasarar APC a zabukan shekarar 2023.” In ji Gusau.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya