✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ma samun isasshiyar wutar lantarki sai in ka zo – Dattawan Daura ga Buhari

Dattawan yankin Daura a  Masarautar Daura da ta kunshi kananan hukumomi biyar, sun sanar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cewa kawai suna samun isasshiyar wutar…

Dattawan yankin Daura a  Masarautar Daura da ta kunshi kananan hukumomi biyar, sun sanar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cewa kawai suna samun isasshiyar wutar lantarki ce idan ya shiga garin.

Dattawan sun bayyana haka ne a lokacin da suka kai wa Shugaba Buhari ziyarar Barka da Sallah a gidansa da ke Daura.

Daya daga cikin dattawan, Mohammed Saleh ya ce, “Duk lokacin da Shugaban Kasa yake gari muna samun wutar lantarki isasshiya. Amma idan ba ya gari, wutar lantarkin kuma sai dai abin da muka samu.”

Daga nan sai ya yaba wa Shugaba Buhari kan sanya hannu a dokar kafa Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Tarayya a Daura bayan sun yi koken cewa an bar yankin a baya wajen makarantu gaba da sakandare, wanda samun makarantun a yankin zai taimaka wajen nusar da matasan yankin su ci gaba da karatu.

Wani jagora a yankin, Yusuf Bello Mai’aduwa godiya ya yi ga mutanen Najeriya bisa yadda suka sake aminta da Shugaba Buhari har suka sake ba shi damar ci gaba da jan ragamar mulkin kasar nan a karo na biyu, inda ya ce yana tabbacin Shugaba Buhari ba zai ba su kunya ba.

Da take nata jawabin, Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Watsa Labarai ta ce Shugaba Buhari ya taimaka wajen karfafa wa mata gwiwa, inda yanzu haka da yawa daga cikinsu suke harkokin kasuwanci da suka hada da noman zamani da kiwo.

Da yake mayar da jawabi, Shugaba Buhari ya ce zai bakin kokarinsa wajen ganin ya kwato wa talaka ’yanci.

Shugaba Buhari ya ce yana jin dadi yadda da yawa daga cikin mutanen Najeriya suka gane shi wane ne, da salon mulkinsa da kuma inda ya dosa, wanda hakan ya sa suka sake amincewa da shi har suka sake zabensa karo na biyu domin ya ci gaba da mulki.

“Lallai, mutanen Najeriya sun fahimci inda muka dosa a salon mulkinmu. Wannan shi ne za a fahimta daga yadda aka yi mana ruwan kuri’a a zaben da ya gabata. Don haka za mu ci gaba daga inda muka tsaya, musamman abubuwan da muka yi alkawari a lokacin yakin zabe, inda muka yi ta nanata cewa za mu mayar da hankali kan abubuwa da suka shafi tsaro da tattalin arziki da yaki da cin hanci. Don ba makawa, za mu ci gaba da nema wa talaka ’yanci,” inji shi.

Shugaban ya kara da cewa harkokin noma na da matukar muhimmanci a gwamnatinsa, sannan ya yi alkawarin zaben Ministan Noma da ya kware a harkar noma domin samun inganci a bangaren.

Daga nan sai mutanen yankin na Daura suka gabatar da addu’o’i ga Shugaban, sannan suka bukaci ya ci gaba da kokarin da yake yi domin gyara Najeriya ta hanyar tsayawa kan gaskiya, kuma ya ci gaba da lura da bukatun talaka.