Da Dumi Dumi

Ba ma yin kafar ungulu ga neman maganin Zakzaky – Indiya

India, ta yi watsi da batun jinyar da ake yadawa game da shugaban Kungiyar Shi’a Sheikh Ibrahim Zakzaky, inda bayanan ke cewa, kasar na yi wa neman maganin Zakzaky kafar ungulu.

Sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa, Zeenat, na kasar ta Indiya, don neman magani, biyo bayan belin da aka ba su domin jinya.

Sai dai kungiyar ta ‘yan Shia ta yi zargin jami’an Najeriya da kuma na Amurka, sun hade baki wajen hana jagoran nasu damar ganin likitocin da za su duba lafiyarsa.

Ofishin jakadancin Indiya a Najeriyar ya bayyana cewa, ‘Babu wasu sharuddan da aka gindaya wa Zakzakyn da mai dakin nasa game da neman maganin da suke yi ko kuma wa’adin da Indiyan ta basu da su bar kasar.

ADVERTISEMENT
Share