✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba matsalar da za ta hana mu gudanar da zabe a wannan wata – Hukumar Zaben Jigawa

Sakataren Hukumar Zabe ta Jihar Jigawa Alhaji Sani Ahmed Gumel ya musanta labarin da ake yadawa cewa hukumar tana cikin matsalar karancin kudi da zai…

Alhaji Sule Lamido Gwamnan Jihar JigawaSakataren Hukumar Zabe ta Jihar Jigawa Alhaji Sani Ahmed Gumel ya musanta labarin da ake yadawa cewa hukumar tana cikin matsalar karancin kudi da zai hana ta aiwatar da zaben kananan hukumomin jihar a lokacin da ta tsara, inda ya ce gwamnatin jihar ta ba su isassun kudin da za su aiwatar da zaben a lokacin.
Alhaji Sani Gumel ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin wakilinmu inda ya ce gwamnatin jihar ta ba hukumar sama da Naira miliyan 500 wadanda da su ne za su yi aikin zaben kananan hukumomin da suke sa ran yi a wannan wata.
Ya kara da cewa sun amshi kudin daga hannun gwamnatin jihar tun watan Satumbar da ya gabata kuma tuni suka dauki ma’aikatan wucin-gadi sama da dubu 10 daga kananan hukumomin jihar 27 wadanda mafi yawansu ma’aikatan kananan hukumomin ne yayin da wasu kuma malaman firamare ne.
Ya ce ma’aikatan hukumar sun samu horo daga wata hukuma mai zaman kanta ta kasar Amurka da ta yi fice a kan yadda ake samun zabe mai inganci.
Sakataren ya ce jam’iyyu 22 ne za su shiga zaben kananan hukumomin inda Jam’iyyar PDP ta tsayar
da ’yan takarar shugabannin kananan hukumomi 27 da kansiloli 287, yayin da APC ta tsayar mutum bakwai a takarar kujerun ciyamomi da kuma kansiloli 44.
An dai rika yada jita-jita a jihar cewa zai yi wuya hukumar ta gudanar da zaben a ranar 18 ga Janairun nan, sakamakon karancin kudi da hukumar take fuskanta.