✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu amince da PDM a matsayin jam’yyar siyasa ba – Matawallen Hadeja

Alhaji Abdullahi Abdulkadir Mohammad (Matawallen Hadeja) shi ne Kodinatan Shiyyar Arewa maso Yamma na kungiyar PDM wacce hukumar zabe ta yi wa rajista a matsayin…

Alhaji Abdullahi Abdulkadir Mohammad, Matawallen HadejaAlhaji Abdullahi Abdulkadir Mohammad (Matawallen Hadeja) shi ne Kodinatan Shiyyar Arewa maso Yamma na kungiyar PDM wacce hukumar zabe ta yi wa rajista a matsayin jam’iyyar siyasa a makon jiya. Sai dai wasu mambobin kungiyar ta PDM a Arewa maso Yamma sun yi taron gaggawa a Kaduna inda suka ce su ba su yarda da wannan rajista da aka yi ba. Aminiya ta zanta da Matawallen domin jin dalilinsu na kin yarda da rajistar:

Aminiya: Mene ne makasudin wannan taro na kungiyar PDM sashin Arewa maso Yamma a nan Kaduna?
Ni na kirawo wannan taro na kodinatocinmu na jihohi bakwai da ke wannan yanki namu da kuma sauran shugabanninta. Muka zauna muka tattauna maganar rajistar da aka ce an yi wa PDM. Abin da taronmu ya yarda, shi ne cewa gaba daya mu jihohin Arewa maso Yamma ba ma goyon bayan rajistar da aka yi wa PDM ba a matsayin jam’iyyar siyasa. Amma muna nan a cikin kungiyar PDM wanda ba jam’iyya ba, sai dai ba mu yarda da rajistarta a matsayin jam’iyya. Dalili shi ne saboda ba a tuntubi kowa ba lokacin da ake neman rajistar nan, wasu ’yan tsirarun mutane ne su shida suka je suka shirya wannan abu. Suka kuma nemi rajistar ba tare da jin ra’ayoyinmu ba.
Ni din nan ina cikin shugabannin zartarwa na kasa wadannda mu ne kamar shugabanninta na kasa, su kuma wadanda suka yi abin wasu ’yan kwamiti ne. Saboda haka ba su da ikon yin wani abu sai mun amince. Ni kaina a bakin wani na ji ba ma a rediyo ko jarida ba. A bakin wani na ji wai an yi mata rajista amma duk da haka abu ne ake yi na jama’a, tunda kungiya ce dole ne a kirawo mutane domin jin ra’ayinsu daga jihohi bakwai da ke a wannan yanki namu. Saboda haka a yanzu abin da taron nan namu ya zartar shi ne cewa yana cikin PDM kungiya ba PDM jam’iyya ba. Kuma mafi yawanmu ’yan Jam’iyyar PDP ne kuma muna nan a PDP abinmu. Ba mu fita a PDP ba. Wannan shi ne abin da muka yarda da shi kuma shi ne wannan taro ya zartar da shi.
Aminiya: Ita dama can PDM kungiya ce ta siyasa ko ba ta siyasa ba?
Da ma kungiya ce ta siyasa domin kusan a karkashin Jam’iyyar PDP take. Wanda ya kafa wannan kungiya shi ne marigayi Shehu Musa ’Yar’aduwa. Ya kafa PF aka nemi rajista da ita a lokacin mulkin Janar Babangida, ya hana rajistar inda ya soke kungiyoyin siyasa, ya kafa jam’iyyu biyu kawai wato NRC da SDP.  Sannan daga baya lokacin Janar Abacha aka kafa kungiyar PDM. Ai wannan PDM ita ce uwar PDP daga sunanta aka fito da sunan PDP.
Aminiya: Ba ka ganin wasu za su ce an turo ku ne domin ku kawo kafar ungulu cikin harkar?
Babu wani zancen kawo kafar ungulu, idan ma zancen kawo kafar ungulu ce ai wadannan mutane shida su suka kawo. Ta yayi za a ce mutum shida ne kawai za su tafiyar da ra’ayoyin ’yan Najeriya gaba daya. Mutum shida ne kawai za su rinjayi ’yan Najeriya gaba daya, ai ba mulkin kama-karya ake yi ba dimokuradiyya ake yi.  A tsarin dimokuradiyya ana son a samu yardar mafi rinjayen mutane kafin ka yi wani abu kamar dai yadda muka yi a yanzu.
Aminiya: Ga alama dai a yanzu kun ja layi ke nan?
kwarai kuwa munja layi, domin su suna PDM jam’iyya mu kuma muna PDM kungiya. Kuma a haka za mu ci gaba da tafiya.