Da Dumi Dumi

Ba mu bukatar fina-finan Indiya a Ramadan – Saudi Gazette

Wasu gungun masu kallon fina-finai a Saudi Arebiya sun barranta kansu da tashar talabijin din satalayit ta Zee Aflam, mai nuna fina-finan Indiya a duniya.
Kamar yadda mujallar Saudi Gazette ta ruwaito, a sakamakon sanarwar da tashar ta Zee Aflam ta bayar, inda ta sha alwashin nuna zababbun fina-finan Indiya ga masu kallo a cikin Ramadan, mai magana da miyan mutanen ya ce: “Mun samu sanarwar Zee Aflam, na shirin haska zababbun fina-finan Indiya a watan Ramadan cikin takaici da bakin ciki. Ya kamata masu gudanar da tashar nan su fahimta da cewa Ramadan wata ne na albarka ga al’ummar Musulmi, lokacin da ya kamata mutum ya nisanci aikata ayyukan zunubbai, ya maida hankali wajen ibada da ayyukan kwarai; don haka bai kamata a ce za a dauki hankalin mutane da wannan sanarwa ba.”
Kamar yadda Saudi Gazette ta ci gaba da bayyanawa, tashar Zee Aflam ta sanar da cewa za ta fara nuna fina-finan ne tun daga karfe 7:00 na dare har wayewar gari. “Wannan zai shagaltar da mutane su kasa gudanar da sallolin Tarawi da sauran muhimman ibadojin dare cikin watan. Ai tashar an san ta da nuna fina-finan Indiya a duk tsawon shekara, amma wane dalili ya sanya ta ware watan Ramadan, wajen yin talla da sanarwar musamman game da fina-fnan da za ta nuna? Wannan wani salo ne na wulakantawa da kaskantar da al’ummar Musulmi.” Inji Muhammad Jamil, mai magana da miyan al’ummar da suka la’anci yunkurin tashar.
Daga karshe, jami’in ya ja hankalin shugabannin tashar da su yi la’akari da watan Ramadan, sannan su fahimta da cewa Saudi Arebiya cibiya ce ta addinin Musulunci, wadda ita ce mahaifar Manzon Allah (SAW), wadda ke dauke da muhimman masallatan duniya guda biyu. “Ina fata za su janye wannan sanarwa, sannan su dakatar da shirinsu na nuna wadannan zababbun fina-finai a wannan lokaci mai muhimmanci ga al’ummar Musulmi.” Inji shi.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya