✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu da matsalar fansho sai ta garatuti  – Muhammad Abubakar

A daidai lokacin da Gwamnatin Jihar Gombe ta fara biyan ma’aikatan da suka yi ritaya a shekarar 2014 garatutinsu, Shugaban Kungiyar ’Yan Fansho ta Jihar…

A daidai lokacin da Gwamnatin Jihar Gombe ta fara biyan ma’aikatan da suka yi ritaya a shekarar 2014 garatutinsu, Shugaban Kungiyar ’Yan Fansho ta Jihar Gombe Alhaji Muhammad Abubakar ya ce gwamnati na biyansu fanshonsu a kan lokaci ba sa bin bashi sai dai na garatuti.

Alhaji Muhammad Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin wakilinmu a Gombe inda ya ce su tsofaffin ma’aikata ba su da matsala kan biyan fansho abin da suke so shi ne gwamnati ta biya su sauran garatutinsu.

Ya ce wadanda ake biya garatuti su fiye da 500, sun bar aiki ne a shekarar 2014, kuma rabi-rabi ake biyansu ba duka ba. Ya ce nan ma ma’aikatan jiha ne babu na kananan hukumomi a cikinsu duk da cewa tun daga shekarar 2013 nasu ya fara ba shekarar 2014 kamar na ma’aikatan jiha.

Shugaban ya ce a lokacin da ya zama shugaba a shekarar 2014 ya sa aka gyara musu albashin nasu na fansho domin da mafi karancin abin da ake biyansu shi ne Naira 4,500 amma yanzu Naira 9,000 ne mafi karancin abin da ake biyansu.

Ya ce wadanda ake biya din ma wadanda suka tashi ne suka bi fayel dinsu har zuwa ofishin fansho, wadanda ba su bi na su ba ba sa cikin wadanda ake biya.

“A madadin ’yan fansho na kananan hukumomi, muna kira ga Gwamna Inuwa Yahaya ya biya tsofaffin ma’aikatan kananan hukumomi su ma saboda suna da yawa kuma su ne suka fi zama abin tausayi,” inji Abubakar.

Ya gode wa Gwamnan kan yadda a yanzu ya waiwaiye su don rage musu wahala duk da cewa rabi ake biyansu ba duka ba, “hakan ma ya kyauta,” inji shi.

Daga nan sai ya ce shugabaninsu a matakin kasa suna bin sawun lamarin domin ganin gwamnati ta kara musu abin da suke karba na fansho kamar yadda ake kara wa ma’aikata albashi a wasu lokuta.