✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu ga zama ba- Buratai

Babban hafsan Sojan Najeriya Laftanar Janaral Tukur Buratai ya yi kira ga sojojin da ke Jihar Yobe a yankin Arewa maso Gabas da suke kara…

Babban hafsan Sojan Najeriya Laftanar Janaral Tukur Buratai ya yi kira ga sojojin da ke Jihar Yobe a yankin Arewa maso Gabas da suke kara kaimi wajen ganin sun murkushe sauran burbusihn ‘yan Boko Haram.

Buratai ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake ganawa da jami’an sojin sashe na 3 a Damauru da ke Jihar Yobe, inda ya ce lallai ba su ga hutu ba har sun ga karshen ‘yan ta’addan.

Buratai ya kara da cewa manyan hafoshin sun dira a Maiduguri ne saboda biyayya da umarnin da mukaddashin shugaban kasa ya yi. Sannan ya tabbatar da cewa za su hada karfi da karfe wajen ganin an samu nasara cikin sauri.

Buratai wanda ya samu rakiyar manyan jami’an Soji, ya zanta na dogon lokaci da sojojin yankin domin jin ta bakin su.