✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu goyon bayan dawowar Gwamna Matawalle Jam’iyyar APC – Musa Gusau

Bayanan da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Ahmad Yariman Bakura ya yi kan yiwuwar dawowar Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle jam’iyarsu ta APC sun…

Bayanan da tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Sanata Ahmad Yariman Bakura ya yi kan yiwuwar dawowar Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Bello Matawalle jam’iyarsu ta APC sun haifar da cece-ku-ce a tsakanin wadansu ’ya’yan jam’iyyar da ke ganin haka ba za ta sabu ba.

Sakataren Kungiyar Matasa Masu Kishin Jihar Zamfara Alhaji Musa Gusau ya ce magoya bayan Jam’iyyar APC sun ga tattaunawa da Aminiya ta yi da Sanata Sani Yariman Bakura inda yake cewa Gwamna Bello Matawalle yana dab da dawowa a jam’iyyar, inda ya ce, “Hakika wannan ba abin mamaki ba ne idan aka ce wannan bayani ya fito ne daga bakin tsohon Gwamnan.

Sakataren a zantawarsa da Aminiya ya ce  yana da kyau Yariman Bakura ya san cewa al’ummar Jihar Zamfara musamman magoya bayan Jam’iyyar APC tuni sun yi watsi da duk wani salo na siyasarsa, sun rungumi tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari a matsayin jigon Jam’iyyar APC a Jihar.

Ya ce akwai zarge-zargen da ake yi wa Sanata Yarima na  zama silar dukkan wasu matsaloli da Jam’iyyar APC ta fuskanta a zaben bara, tare  da goyon bayan ’yan Kungiyar G-8 don tarwatsa Jam’iyyar APC a Zamfara.

“Yanzu  kuma sai ga  wannan yunkuri nasa na dawowa da Gwamna Bello Matawalle zuwa Jam’iyyar APC, saboda wani kuduri nasa da kuma shirye-shiryensa na takarar Shugaban Kasa a zaben 2023,” inji Sakataren.

Ya ce abin takaici ne duk irin zalunci da cin zarafi da Gwamnatin Bello Matawalle take yi wa magoya bayan Jam’iyyar APC a Zamfara, a ce Sanata Yarima ya aminta da kudIrin  dawo da Gwamna cikin APC.

“Ba ma ganin akwai wani yunkuri da zai hana tsohon Gwamna Abdul’aziz Yari  zama Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa, bayan dukkansu sun fahimci tabbaci da bayanai na cewar dukkan masu fada-a-ji a Jam’iyyar APC da dattawan Najeriya suna ba da goyon baya wajen tabbatar da tsohon Gwamnan  a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC ta Kasa don samun nasarar APC a zabubbukan shekarar 2023,” inji Gusau.