✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu hade wa Buhari baki ba – Babangida

Tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya gasgata wasikar da aka ce ya rubuta game da adawa da sake zaben Buhari…

Tsohon Shugaban Kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya gasgata wasikar da aka ce ya rubuta game da adawa da sake zaben Buhari a wa’adi na biyu.

A watan Fabrairu ne aka wallafa wata wasika da aka ce ta fito daga tsohon Shugaban inda a ciki ya bukaci shugaba Buhari ya janye neman wa’adin shugabanci na biyu, ya ba matasa dama.

Daga baya Janar Babangida ya musanta cewa shi ya rubuta wasikar, amma a wata hira da aka yi da shi wacce aka wallafa a jaridar Premium Times ta Intanet a ranar Lahadin da ta gabata, tsohon Shugaban Kasar ya amsa daukar alhakin rubuta wasikar, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Janar Babangida ya ce ’yan jarida ne suka sauya asalin abin da ya fada a cikin wasikar bayan an tambaye shi dalilin da ya sa, shi kuma ya musanta bayan fitar da wasikar.

Tsohon Shugaban ya ce ’yan jarida ya zarga, domin abin farko da wani ya ce, “IBB ya ce Buhari ya yi tsufa da zama Shugaban Kasa, ko wasu kanun labaran da ba su dace ba da za su gama ni fada da Shugaban Kasa. Ba na son shiga fada kan abin da ban ce ba.”

Mai magana da yawun tsohon Shugaban Kassim Afegbu ne ya fitar da wasikar, kuma a ciki ya yi kira ga Shugaba Buhari da kada ya tsaya takara a zaben 2019.

Amma daga baya Babangida ya ce, “Bayanan da aka fitar a cikin wasikar da aka danganta da ni ba nawa ba ne.”

Ya ce, “Babu wani shinge a tsakanina da masu rike da madafan iko a Najeriya.”

Kafin Babangida ya fitar da wasika game da sake zaben Buhari, tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo da Janar Theophilus Danjuma sun rubuta wasikar nuna adawa da gwamnatin Buhari.

An tambayi Babangida, ko hakan yana nufin dukansu tsofaffin shugabannin soja sun hade wa Buhari baki ne kafin zaben 2019? Sai ya ce ’yan jarida ne kawai suka kirkiri haka.

Ya ce bayan Janar Obasanjo da Janar Danjuma sun rubuta wasikarsu, kafin ya rubuta tasa, kawai sai ’yan jarida suka yanke hukunci cewa sun hade wa Buhari baki ne. “Babu wani hada baki, kawai tunanin ’yan jarida ne,” in ji Babangida.