✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba mu ji dadin fitowa takarar Gwamna da kwamishinanmu ya yi ba – INEC

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ba ta ji dadin yadda Kwamishinan Zabe na Jihar Kuros Riba Dokta Frankland Briyai ya fito neman tsayawa…

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ba ta ji dadin yadda Kwamishinan Zabe na Jihar Kuros Riba Dokta Frankland Briyai ya fito neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Bayelsa a zaben da ke tafe na ranar 16 ga Nuwamba ba.

A amkon jiya ne a wani taron manema labarai, Dokta Briyai ya sanar da niyyarsa ta shiga wata jam’iyyar siyasa don a fafata da shi wajen neman tsayawa takarar Gwamnan Jihar Bayelsa, inda ya ce takarar tasa ta fara ne tun daga ranar 8 ga watan Agusta.

Hukumar INEC ta ce duk da cewa Dokta Briyai ya bayyana niyyar tsayawa takarar ce a ofishin hukumar da ke birnin Kalaba, amma har yanzu ba su samu wata takarda daga wurinsa ba dangane da takarar tasa.

Wannan al’amari bai yi wa Hukumar INEC dadi ba kamar yadda ta ce a wata sanarwa da ta fitar. “Hukumar INEC ba ta ji dadin niyyar Kwamishinan Zabe na Jihar Kuros Riba ba, ta shiga siyasa. Saboda tsarin mulki ya hana ma’aikacin hukumar zabe shiga wata jam’iyyar siyasa.”

Sanarwar wadda ke dauke da sa hannun Kwamishinan Hukumar INEC Mai kula da wayar da kan jama’a, ta kara da cewa, “Yin amfani da farfajiyar ofishin hukumar da kayan hukumar ya saba doka sannan bai bi tanade-tanaden dokokin da’ar ma’aikata ba, da ya kamata a ce duk jami’in Hukumar INEC yana bi sau da kafa.”

Kwamishinan ya ce jami’in nasu bai, bi ka’idojin hukumar ta gindaya na barin aiki ba.

Tuni dai Hukumar INEC ta kori kwamishinan da yake neman tsayawa takarar Gwamnan, inda ta umarci Sakataren Gudanarwar Hukumar ya karbi ragamar shugabancin hukumar a jihar.