Da Dumi Dumi

Ba na goyon bayan dakatar da Jonathan –  Lamido

Alhaji Sule Lamido
Alhaji Sule Lamido

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce ’yan siyasa sun saba yaudarar jam’iyyarsu. Tsohon Gwamnan ya ce irin wannan abu ba bako ba ne a tafiyar PDP. Alhaji Sule Lamido ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya yi hira da wata ba Aminiya ba game da zaben Gwamnan Jihar Bayelsa da aka yi kwanan nan, wanda Jam’iyyar PDP ta sha kaye. Yayin da yake magana game da kiran da ake yi na a dakatar da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan daga jam’iyyar, ya ce wadansu sun yi fiye da abin da Jonathan ya yi… yaudara ita ce tambarin PDP. A wurina Jonathan yana cikin kura-kuran da Obasanjo ya tafka wa Najeriya. Ba na ganin cewa ya kamata a hukunta Jonathan a kan abin da ya yi. Sam yin hakan bai da wata ma’ana,” inji shi.

Lamido ya ce mutanen da suke gaba da Jonathan, suka girme shi, sun yi abin da ya zarce nasa, sun yi abin da ya fi wanda ya yi muni. Don haka Jonathan ya yi abin da manyansa a harkar siyasa da jagoranci suka yi. Kusan kashi 80 na ’yan siyasar APC sun fito ne daga cikin PDP, duk kun san wannan. Duk wanda yake wani abu a majalisa tsakanin 1999 zuwa 2015, ya yi Jam’iyyar PDP,” inji Alhaji Sule Lamido.

Ya ce “Duk wanda yake cikin gidan gwamnati a matsayin wani babba a yau, ya yi PDP.”

Ya ce saboda haka yaudara a jinin Jam’iyyar PDP take.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya