✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba na neman matsayin Shugaban Masu Rinjaye – Wamakko

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltaar mazabar Sakkwato ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko ya karyata labaran da wasu jaridu suka buga, na cewar ya na neman…

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltaar mazabar Sakkwato ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko ya karyata labaran da wasu jaridu suka buga, na cewar ya na neman mukamin shugaban masu rinjaye a majalisar ta dattawa.

Ya ce shi ba ya neman kowanne irin mukami a cikin majalisar,  a cewarsa, “Bani da sha’awar neman mukamin shugaban majalisa, ko makamancin hakan, kuma ni ban shiga takarar nema ba,’’ a sanarwar da mataimakin na mussaman akan harkokin yada labarai ga Sanata Wamakko, Bashir Rabe Mani tana cewa duk labarin da jaridu suka buga na cewar yana neman mukamin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan karo na 9 ba bu gaskiya a cikinsa.