Da Dumi Dumi

Ba ni ba siyasa – Sanata Adokwe

Sanata Suleiman Asonya Adokwe
Sanata Suleiman Asonya Adokwe

Sanata Suleiman Asonya Adokwe ya ce ya ajiye siyasa. Hakan na zuwa ne bayan tsohon Sanatan na Nasarawa ya gaza karbe kujerarsa a kotun karar zabe. Sanata Suleiman Adokwe ya wakilci Nasarawa ta Kudu a Majalisar Dattawa a karkashin Jam’iyyar PDP. Tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Umaru Tanko Al-Makura ne ya samu nasara a kansa a zaben da aka gudanar a bana.

Adokwe ya ce “A shekaruna yanzu a duniya ba zan iya zuwa ina neman kujerar siyasa ba. Na kai matsayin da zan zama dattijo, amma tsayawa takara ba ya cikin lissafina a yanzu.” Sanatan ya nuna cewa ya amince da shari’ar da kotun ta yi inda aka tabbatar da nasarar Sanata Umaru Tanko Al-Makura a matsayin Sanatan Kudancin Nasarawa.

Sanata Adokwe ya bayyana cewa bai da ja da zabin da UbangijiYa yi a shari’ar da ya daukaka, ganin cewa ya yi aiki a Majalisar Dattawa na shekara 12.

Sau uku ana zaben Sanata Adokwe a matsayin dan Majalisar Dattawa. Sai dai a wannan karo ne ya sha kaye a hannun tsohon Gwamna Umar Tanko Al-Makura na Jam’iyyar APC. Tsohon Sanatan na Nasarawa ta Kudu ya shigar da kara a kotu yana kalubalantar nasarar da APC ta samu. Sanatan bai yi nasara ba, don haka ya daukaka kara, inda a nan ma aka ba APC gaskiya.

ADVERTISEMENT
Share