✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba ni da shirin yin takarar Sanata- Makarfi

Tsohon shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar PDP Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, ya musanta rahotan dake bayyana cewa, yana da aniyar yin takarar Sanata a…

Tsohon shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar PDP Sanata Ahmed Mohammed Makarfi, ya musanta rahotan dake bayyana cewa, yana da aniyar yin takarar Sanata a 2019.

Sanata Makarfi ya yi takarar zaben fidda gwani na neman tikitin  yin takarar Shugaban Najeriya, inda tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya lashe zaben.

Maitaimakawa Sanata Makarfi akan sadarwa, Mukhtar Sirajo ne ya sanar da hakan inda ya ce Sanata Makarfi bai da wannan aniyar tsaya wa takarar Sanata a zaben 2019.