✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba Ruwan Dan Takarar Gwamnan Taraba Da Badakalar Miliyan 450 Na Kamfe – APC

Jam’iyyar APC reshen Jahar Taraba ta maida martini game da karar da Hukumar EFCC ta shigar gaban kotu, inda ta ce ta na mamakin yadda…

Jam’iyyar APC reshen Jahar Taraba ta maida martini game da karar da Hukumar EFCC ta shigar gaban kotu, inda ta ce ta na mamakin yadda wasu ke nacewa akan sai an gurfanar da dan takarar ta na gwamna a zabe mai zuwa, Sanata Sani Abubakar Danladi, kan badakalar Naira Miliyan 450, da tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan ta bayar na kamfe din 2015.

A martanin da jam’iyar ta mayar na cece-kucen da ke faruwa game da karar da hukumar EFCC ta shigar a babban kotun tarayya na wadanda ake zargin sun karbi wadannan kudade, jam’iyar ta APC ta yi zargin cewa wasu ne ke neman shafa wa dan takararta kashin kaji.

Mai Magana da yawun Jam’iyar APC na Jihar Taraba, Misata Aron Arthimas, ya ce dan takarar su Sanata Sani Abubakar Danladi bai dauki kudin bisa kansa ba. Wasu sanatoci biyu ne su ka sa hannu su ka karbi kudin a lokacin, sannan a lokacin ya na rikon gwamnan jahar ya kafa kwamiti na mutum takwas, wadanda suka jagoranci raba kudin zaben.

Wani lauya mai zaman kansa a Jalingo, Barista Idris Abdullah Jalo ya bayyana abunda doka ta ce, inda ya ce ba a fahimci lamarin ba ne, saboda har yanzu fa wanda ake tuhuma ba a bashi takardar tuhuma ko ta gayyata ba domin ya bayyana a gaban kotu, sannan wadanda suka kawo karar wato hukumar EFCC ba ta kawo kararsa ba.