Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ba sai mace tana da babban jari za ta fara kasuwanci ba –Hajiya Fatima Usman

Hajiya Fatima Bintu Usman
Hajiya Fatima Bintu Usman

Wata ’yar kasuwa a Jihar Kano, Hajiya Fatima Usman da ta shafe shekara 20 tana gudanar da kasuwanci ta bayyana cewa ba sai mutum ya samu babban jari ko ya bude shago sannan zai fara kasuwanci ba. ’Yar kasuwar ta shaida wa Aminiya cewa ana iya fara kasuwanci da jarin da bai kai ya kawo ba.

“Lokacin da na fara kasuwanci na fara da kudi dan kadan. Ina zuwa kasuwa in sari kaya in sayar a cikin gidana. sai dai da yake Allah Ya sa wa abin albarka sai aka wayi gari ya bunkasa. Tun ina sayar da kaya a gida ya zamo an wayi gari ina zuwa Legas in kawo kaya  in sayar. Ya zama muka bude dan karamin shago muna sayar da kaya. To ga shi yanzu mun bude babban shago inda muke sayar da kayayyaki daban-daban, alhamdulillah,” inji ta.

ADVERTISEMENT

A cewar Hajiya Fatima abin da mutum yake bukata kafin fara kasuwanci shi ne hakuri da juriya da jajircewa. “Dole sai mutum ya yi hakuri ya jajirce. Yayin da mutum ya fara ba lallai ne ya samu ciniki da yawa ba, to a nan mutum sai ya nace ya ci gaba da yi. Kada ya yarda ya sare ya daina. Idan kana yi yau da gobe za a rika ci gaba. Mu ma da haka muka fara. Akwai batun bashi, musamman a wannan zamani zai yi wuya a ce za a yi kasuwanci ba tare da bashi ba. A mafi yawan lokuta za ka ga jama’a na yi wa mutum wasa da kudi wajen kin biya a kan lokaci, to dole sai mutum ya yi hakuri, sannan komai zai tafi daidai,” inji ta.

Ta ce da mata za su gane sirrin kasuwanc ba za su taba yarda su fara ko su ci gaba da aikin albashi ba.

ADVERTISEMENT

Hajiya Fatima, ta ce babban  kalubalen kasuwanci shi ne yadda mutum zai rike abokan cinikinsa “Akwai gasa a kasuwa, ma’ana mutane da yawa suna sayar da irin abin da kake sayarwa, don haka dole mutum ya dage ya rike abokan cinikinsa. Wannan ba zai yiwu ba sai  mutum ya dage wajen kawo wa musu kayan da suke so masu inganci . Wannan shi ne hanyar da muka bi muke samun nasara, wato muna kokarin samar wa abokan ciniki abin da suke so. Ba yadda za ka sayar wa mutum abu mara inganci gobe ya dawo wurinka. Dole ka yi tunanin yadda za ka saye zuciyar abokan hulda,” inji ta.

Ta yi kira ga matasa su daina jiran aikin gwamnati, su nemi yadda za su fara kasuwanci ko sana’a “Ya kamata matasa su fahimci cewa ba kowa ba ne zai sami kudi da biro, don ka yi karatu ba shi yiwuwa ka ce dole sai ka yi aikin gwamnati. Idan mun duba kullum gwamnati korafi take ba ta da guraben aiki don haka dole ne mu nema wa kanmu mafita ta hanyar samar wa kanmu aiki,” inji Hajiya Fatima.