✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba shugaban da zai yi farin ciki a Arewa – Sarki Sanusi

Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ll ya bayyana cewa babu wani shugaban daga Arewa da zai yi farin ciki kan halin da yankin yake…

Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi ll ya bayyana cewa babu wani shugaban daga Arewa da zai yi farin ciki kan halin da yankin yake ciki, a daidai wannan lokaci da Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 87 na talauci a Najeriya yana yankin Arewa ne.

Sarkin ya ce rahoton ya bayyana akalla jihohin Arewa tara ne ke samar da kashi 50 cikin 100 na cutar tamowa a kasar nan baki daya.

Sarkin wanda ke jawabi a wajen bikin taya Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i murnar cika shekara 60 a duniya a Kaduna ya ce babu wani shugaba a yankin Arewa da yake farin ciki idan ya yi la’akari da halin da yankin ke ciki a yanzu.

Sarkin ya kuma ce idan har yankin Arewa bai canja yadda yake gudanar da ayyukansa ba zai hallaka kansa da kansa.

”Idan muna batun bikin murnar haihuwa, muna batun farin ciki ne, a makon da ya wuce wani ya tambaye ni ko ina farin ciki? Sai na ce masa a’a. Sai ya kasance cike da mamaki.  Babu wani shugaba a Arewacin Najeriya a yau da zai kasance cikin farin ciki. Babu yadda za ka yi farin ciki da cewa kashi 87 na talauci na yankin Arewa. Ba za ka yi farin ciki da ganin miliyoyin yaran Arewa ba su zuwa makaranta ba. Ba za ka yi farin ciki da jihohi 9 na Arewa na samar da kashi 50 na cutar tamowa a kasar nan ba,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Ba za ka kasance cikin farin ciki da matsalolin kwayoyi ba, ba za ka kasance cikin farin ciki da ’yan Boko Haram ba. Haka ba za ka kasance cikin farin ciki da ’yan bangar siyasa ba, kuma ba za ka kasance cikin farin ciki da matsalar almajiranci ba. Mun sha fadin wadannan kalamai shekara 20 zuwa 30 da suka wuce. Idan har Arewa ba za ta canja yadda take gudanar da al’amuranta ba za ka hallaka kanta.”

Sarkin ya bayyana cewa, “Kana kasancewa cikin farin ciki ne idan a matsayinka na shugaba ka ciyar da al’ummarka gaba wato ka kai su inda ya kamata a kai Su.”

Ya yaba wa Gwamna El-Rufa’i kan yadda yake tafiyar da mulkinsa ta hanyar bai wa matasa damar bada gudunmawarsu a harkar mulki. Ya ce dole a tashi tsaye wajen inganta rayuwar matasan yankin domin su kasance masu dogaro da kansu tare da ciyar da yankin Arewa da kasa gaba.