✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za a taba daina garkuwa da mutane ba – Gwamna Wike

Gwamnan JIhar Ribas, Mista Nyesom Wike ya ce satar mutane da garkuwa da su ba za ta kare ba a kasar nan, domin ta zamo…

Gwamnan JIhar Ribas, Mista Nyesom Wike ya ce satar mutane da garkuwa da su ba za ta kare ba a kasar nan, domin ta zamo wata hanyar samun kudi ga wadansu ’yan tsirarun miyagun mutane.

Gwamna Wike ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata a garin  Fatakwal yayin da ya karbi bakuncin Kungiyar Rotary International District 1941, inda ya ce sai dai kawai a yi abin da za a iya.

“Ba zai taba yiwuwa a daina satar mutane ana garkuwa da su a kasar nan ba, domin ta riga ta zama wata sabuwar harka ko kasuwanci da hanyar samun kudi. Sai dai kawai kowa da kowa a taru a hada kai da gwamnati don ganin an rage ta, amma ba za a iya kawar da ita gaba daya ba.

“Kalli abin da ke faruwa a duk fadin kasar nan, satar mutane ta mamaye kowace jiha, a kwanakin baya ma an sace Alkalin Kotun Daukaka kara a garin Benin, kafin haka, an  sace Alkalin Babbar Kotun Tarayya. Don haka dole ne mu tsaya mu ga mun dakatar da lamarin,” inji shi.

Gwamna Wike ya yi kira ga Kungiyar  Rotary ta fara wayar da kan jama’a, musamman matasa game da illoli da hadarin da ke tattare da garkuwa da mutane da ayyukan kungiyoyin asiri.

Gwamnan ya nemi jama’a su kasance masu lura da ankara a unguwanninsu, tare da daukar matakan kare kansu, musamman lura da cewa barayin mutanen suna amfani ne da ’yan uwa da abokai wajen samun bayanan sirri game da mutum, kafin su sace shi.