✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu bar jirgin Amurka ya wuce ta gabarmu ba – Iran

Shugaban Rundunar Sojin Ruwa ta Iran Admiral Habibullah Seyari ya ce ba za su taba bayar da izini ga jirgin ruwan Amurka samfurin USS John…

Shugaban Rundunar Sojin Ruwa ta Iran Admiral Habibullah Seyari ya ce ba za su taba bayar da izini ga jirgin ruwan Amurka samfurin USS John C. Stennis da ke daukar jiragen sama na yaki ya wuce ta gabarsu ba.

A yayin wani bikin yaba wa sojojin Iran da aka gudanar a Jami’ar Dafus ta Soji, Admiral Seyari wanfa ya amsa tambayoyin manema labarai ya ce, “A baya ba a taba ganin irin wannan jirgi a gabar tekun Basra ba, amma akwai wasu nau’uka daban-daban. Ba za mu taba bayar da izini USS John C. Stennis ya zo kan iyakarmu ba.”

Seyari ya ce Amurka ba za ta iya kalubalantarsu ba, kuma atisayen da suka gudanar na soji na kamar gwada wa Amurkan kwanji ne kamar yadda TRT ya ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labarai na ISNA mallakar Iran ya ruwaito Seyari yana cewa, tura jirgin ruwan yaki da Amurka ta yi zuwa yankin ba ya da wani muhimmanci a wajensu, kuma a shirye suke su kare kasarsu.

Kwana 4 da suka gabata ne jirgin yaki na ruwa na Amurka samfurin USS John C. Stennis ya shiga yankin gabar tekun Basra.

A lokacin da ya shiga yankin, jiragen yakin Iran guda 30 suka yi masa rakiya tare da kada shi zuwa wani wajen wanda bayan haka aka harba makami mai linzami.

Sannan don nuna adawa ga jirgin na Amurka, Iran ta gudanar da wani atisaye a tekun Basra.