✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu kara amincewa da Amurka ba – Shugaban Falasdin

Shugaban Falasdin, Mahmoud Abbas ya ce Falasdinawa ba za su sake amincewa da sa hannun Amurka ba a kokarin samar da zaman lafiya a yankin…

Shugaban Falasdin, Mahmoud Abbas ya ce Falasdinawa ba za su sake amincewa da sa hannun Amurka ba a kokarin samar da zaman lafiya a yankin Larabawa bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana kudus a matsayin babban birnin Isra’aila.

A cewar hukumomi a kasar Falasdin, ayyanawar Trump kuskure ne da zai iya jefa duniya cikin rikici, sannan suka bukaci Majalisar dinkin Duniya ta canja tsarin samar da zaman lafiya a yankin, domin Amurka ba za ta iya jagorantar shirin ba.

“Duk da cewa Falasdinawa suna cikin shirin na samar da zaman lafiya, ba za mu amince da Amurka ba domin ba za su yi adalci ba, domin sun riga sun bata wa Musulmi da Kirista rai a kan birnin kudus.”

Shugaban na Falasdin ya kara da cewa ya kamata a kara kaimi wajen yin sulhu a kan makomar birnin na kudus mai tsarki kamar yadda jaridar Independent ta ruwaito.

Mahmoud Abbas ya yi wannan jawabin ne a taron kungiyar Tarayyar Musulmi na duniya (OIC) na musamman, wanda ya wakana a birnin Istanbul.

Duk da cewa Donald Trump ya ayyana birnin kudus a matsayin babban birnin Isra’ila, kasar Amurka ta nuna cewa za ta ci gaba da shiga tsakani domin kawo zaman lafiya a yankin.