✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu koma PDP ba – Gwamnonin da suka fita

Gwamnoni biyar da suka fice daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC sun shaida wa Shugaba Goodluck Jonathan cewa ficewarsu daga jam’iyyar gaskiya ce ba za…

Gwamnoni biyar da suka fice daga Jam’iyyar PDP zuwa Jam’iyyar APC sun shaida wa Shugaba Goodluck Jonathan cewa ficewarsu daga jam’iyyar gaskiya ce ba za su koma cikinta ba.
Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji  Aliyu Wamakko a madadin Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso (Kano) da Murtala Nyako (Adamawa) da Abdulfatah Ahmed (Kwara) da kuma Rotimi Amaechi (Ribas) ne ya mika sakon haka ga Shugaba  Jonathan a taron zaman lafiya a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja a ranar Lahadi da daddare.
Wamakko ya shaida wa manema labarai na fadar Shugaban kasa da misalign karfe 3:20 na dare bayan tashi daga taron cewa shi da Kwankwaso sun halarci taron ne domin girmama gayyatar Shugaba Jonathan.
“A madadin mu biyar, na riga na shaida wa Shugaban kasa matsayinmu a matsayinmu na Gwamnoni Biyar (G5) cewa mun riga mun fice daga cikin uwar Jam’iy yar PDP, kuma mun riga mun koma wata jam’iyyar. Amma a matsayinsa na Shugaban kasa, idan ya kira mu za mu zo mu saurare shi, kuma mu girmama shi a matsayinsa na jagoran kasarmu. Baya ga haka abin da muka iske a wurin galibi ya shafi harkokin PDP ne,” inji shi.
Gwamna Wamakko ya kara da cewa, “Mun shaida wa Shugaban kasa da Shugaban Kwamitin Amintattun Jam’iyyar PDP matsayinmu. Ba za mu tsaya kan magana kawai ba. Mun zo ne mu gaya musu gaskiya a wurin da ya wajaba a fadi gaskiya, wannan ne dalilin zuwanmu nan.”
Shi da yake magana Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Godswill Akpabio wanda shi ma ya halarci taron ya ce taron ci gaba ne da tattaunawa da Shugaban kasa ya bullo da shi tare da gwamnonin PDP bakwai da aka bata wa rai a watannin baya domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jam’iyyar.
Akpabio ya ce Wamakko mamban PDP daya ne a Jihar Sakkwato, don haka ya fahimci cewa akwai dubban wadanda za su ci gaba da kasancewa a PDP, kuma ya ce ba a tattauna batun APC a taron ba.
Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamna Sule Lamido (Jigawa) da Mu’azu Babangida Aliyu (Neja) da Jonah Jang (Filato) da Mukhtar Yero (Kaduna) da Theodore Orji (Abiya) da Sa’idu dakingari  (Kebbi) da Idris Wada (Kogi) da Ibrahim Shema (Katsina) da Isa Yuguda (Bauchi) da Sulliban Chime (Enugu) da Liyel Imoke (Kuros Riba) da Godswill Akpabio (Akwa Ibom) da Emmanuel Uduaghan (Delta) da Martins Elechi (Ebonyi) da Mukaddashin Gwamnan Taraba Garba Umaru da kuma Shugaban Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar  PDP Tony Anenih.