✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba za mu lamunci hako danyen mai da tsada ba – Ministan Fetur

Ministan a Ma’aikatar Man Fetur, Mista Timipre Sylba, ya bayyana damuwa dangane da yadda Najeriya ke kashe makudan kudade wajen hako danyen man fetur. Minista…

Ministan a Ma’aikatar Man Fetur, Mista Timipre Sylba, ya bayyana damuwa dangane da yadda Najeriya ke kashe makudan kudade wajen hako danyen man fetur.

Minista Sylba ya ce tilas a tashi tsaye a lalubo hanyoyin da za a bi domin rage tsadar hako danyen man fetur a kasar nan.

Ya ce idan aka yi haka, za a kara samun rarar makudan kudaden shiga a cikin asusun Gwamnatin Tarayya, wadanda za ta rika amfani da su tana aiwatar da ayyukan raya kasa da inganta tattalin arziki.

Minista Sylba ya yi wannan bayani ne a Abuja wurin taron gano dabarun rage tsadar hako danyen mai a Najeriya da Hukumar PTDF da KSRBN suka shirya.

Sylba wanda Shugaban Ma’aikata na Ma’aikatarsa, Mista Moses Olamide ya wakilta, ya ce a halin yanzu Najeriya tana kashe Dala 35 kafin ta hako kowace gangar danyen man fetur daya kacal, wannan kuwa ya ce ba abu ba ne mai dorewa.

“Bari in dan yi waiwaye baya. Cikin shekarun 1980 zuwa 1990, Najeriya na kashe Dala 4 kadai wajen hako kowace ganga daya ta danyen mai. Cikin shekarun 2000 kuma tsadar ta daga zuwa Dala 5. Amma a yanzu tsadar ta yi munin da sai an kashe akalla Dala 35 kafin a iya hako kowace ganga daya ta danyen man fetur a kasar nan,” inji shi.

Sylba ya nuna takaicin yadda Najeriya ke kashe makudan kudi wajen hako danyen mai, alhali kasashe kamar Kuwait da Daular Larabawa suna kashe Dala 10 kadai wajen hako kowace ganga daya.

“Don haka a wannan lokaci da ake sayar da kowace ganga daya a kan Dala 50 zuwa 60, bai zai yiwu a ci gaba da kashe Dala 35 kafin a hako ganga daya ta fetur ba,” inji Sylba tare da yin kira a lalubo wasu hanyoyin da za a rage tsadar hako danyen mai a Najeriya.