✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Ba za mu mika wadanda ake zargi ba – Saudiyya

A karon farko an samu bayanai kan yadda dan jarida Jamal Khashoggi ya rika fada wa wadanda suka kashe shi cewa, “Numfashina yana daukewa” a…

A karon farko an samu bayanai kan yadda dan jarida Jamal Khashoggi ya rika fada wa wadanda suka kashe shi cewa, “Numfashina yana daukewa” a daidai lokacin da suke shirin kashe shi a ofishin Jakadancin Saudiyya da ke Istanbul, kamar yadda CNN ta ruwaito.

Kafar labarai ta CNN ta ruwaito daga wadansu da suka tabbatar musu cewa sun karanta cikakken bayanan muryar dan jaridar da aka dauka, Khashoggi ya gane daya daga cikin wadanda suka kashe shi mai suna Janar Maher Mutreb.

Khashoggi ya rika fada masa cewa, “Kada ku yi haka fa. Mutane suna jira a waje.”

Kamar yadda aka ruwaito a baya, budurwarsa ’yar asalin kasar Turkiyya, Hatice Cengiz ta jira Jamal ya fito daga ofishin Jakadancin a ranar 2 ga Oktoba, wanda bai fito ba har aka samu labarin mutuwarsa.

Daga cikin abin da ya rika fada musu akwai, “Ba na iya numfashi,” wanda aka ruwaito ya fada sau uku. Sannan bayanan sun nuna kalmomi da aka jiyo a sautin kamar su “kara” da “datsawa” da sauransu.

Haka kuma majiyar ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa an yi amfani da zarto ne wajen datse kan Khashoggi.

Kuma bayanan sun nuna cewa an gano muryar daya daga cikin wadanda suka yi magana a wajen mai suna Dokta Sala al-Tubaigy, wanda masani ne a bangaren nazari kwakwaf kan dalilin mutuwa da ke aiki da Ma’aikatar Cikin Gidan Saudiyya.

Da suke aika-aikar, an ruwaito Tubaigy yana fada wa sauran mutanen su sanya lasifikar kunne su rika sauraron waka kamar yadda ya yi.

Haka shi ma Mutreb wanda yana daya daga cikin jami’an tsaron Yarima Mohammed bin Salman, an ruwaito shi yana magana ta tarho inda yake bayyana yadda suke gudanar da aikin, sannan a karshe ya ce, “an gama aiki.”

Hukomomi a kasar Turkiyya a makon jiya sun ce suna zargin akwai hannun Saud al-Kahtani wanda na kusa ne sosai ga Yarima Mohammed da kuma Janar Ahmed al-Asiri wajen wannan aika-aikar.

Saboda haka ne Turkiyya ta bukaci a taso keyar wadanda ake zargi daga Saudiyya zuwa Turkiyya domin a bincike su, domin a cewarta, “hakan zai kwantar da hankali matuka.”

A nata bangaren kuma, Saudiyya ta bakin Ministan Harkokin Wajen Kasar, ta bayyana wa manema labarai cewa lallai ba za ta mika wadanda ake zargi zuwa kasar Turkiyya ba duk da cewa Turkiyyar ta bukaci haka.

“A ka’ida ba ma mika ’yan kasarmu ga wata kasa domin su fuskanci hukunci,” inji Ministan Harkokin Wajen Saudiyya Adel al-Jubeir lokacin da yake amsa tambaya game da wadanda Turkiyya ke nema a mika su.

Kasar Amurka, duk da cewa Shugaba Donald Trump ya nuna a fili cewa yana tare da Saudiyya, ta ayyana wadansu mutum 17 ’yan Saudiyya, inda ta kakaba musu takunkumi saboda zarginsu da ake yi, ciki har da Kahtani.

A watan jiya, Ofishin Sauraron Kara na Saudiyya ya sanar da cewa za a yanke hukuncin kisa ga wadansu mutum biyar, sannan kuma mutum 11 cikin 21 da ake zargi suna hannu.