✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Ba za mu zabi Jonathan a Katsina ba – Lawal Kaita

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a Jamhuriyya ta Baiyu Alhaji Lawal Kaita ya ce rabuwar kawuna a Jam’iyarsu ta PDP da warewar Ggwamnonin da ake kira…

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a Jamhuriyya ta Baiyu Alhaji Lawal Kaita ya ce rabuwar kawuna a Jam’iyarsu ta PDP da warewar Ggwamnonin da ake kira G-7 da bayyanar Jam’iyyar APC na iya sa PDP ta gaza yin nasara a zaben 2015, musamman idan aka ce Shugaba Jonathan ya sake tsayawa takara.

Alhaji Lawal Kaita ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Katsina, inda ya ce, “Na san a jiharmu ta Katsina ba za mu yi Shugaba Jonathan a zabe mai zuwa ba, haka Kano da Jigawa wadanda tuni sabuwar PDP ta kafu a cikinsu.
Alhaji Lawal Kaita wanda jigo ne a Jam’iyyar PDP ya kara da cewa,”Hakika, tsarin mulki ya ba kowa damar tsayawa takara muddin ya cika sharudda. To amma mu a PDP wanda ni ina cikin wadanda aka yi wannan tsari da shi mun ce, kowane sashi tsakanin Arewa da Kudu zai yi shugabanci na tsawon shekaru takwas ta yin sau biyu, kuma kowa ya san abin da ya faru da Obasanjo lokacin da ya nemi wucewa karo na uku. Shi kuma wannan sai ya ce sai an rantsar da shi har sau uku? Yayi shekara biyu cikin na Umaru, yanzu yana yin hudu cikin nasa wanda kamata ya yi a ce dan Arewa ne ke yi, to amma saboda tsarin abin da ya ce, in babu shugaba mataimaki ne zai ci gaba. To yana so ne ya yi shekara 10 maimakon takwas na doka, tunda ba mu yarda da shekara 12 ba, a dabarance mana ke nan.”