✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan ba wadanda suka girme ni mukamai ba – Gwamnan Kuros Ribas

Gwamnan jihar Kuros Ribas Farfesa Benedict Ayade, ya ce ba zai kara ba wadanda suka girme shi mukamai ba a gwamnatinsa kuma ya yi nadamar…

Gwamnan jihar Kuros Ribas Farfesa Benedict Ayade, ya ce ba zai kara ba wadanda suka girme shi mukamai ba a gwamnatinsa kuma ya yi nadamar wanda ya bayar a wa’adin mulkinsa na  farko. Gwamna Ayade wanda aka sake rantsar da shi a wa’adin mulki na biyu, yana shan matsin lamba daga tsohon Gwamnan Jihar Sanata Liyel Imoke, a kan ya nada makarraban gwamnatinsa daga magoya bayan tsohon Gwamnan lamarin da  Gwamnan ya ki ya amince, kuma hakan ya sa aka ce yake jan kafa, inda tunda aka kaddamar da shi wa’adin mulki na biyu zuwa yanzu bai nada kwamishinoni da sauran mukamai ba a gwamnatinsa.

Kwanan baya ya gana da tsofaffin kwamishinoni da mataimakansa na musamman da sauran masu ba shi shawara ya mayar da su a matsayin masu kula da ayyukan da ya fara a wa’adin farko bai gama ba kafin ya fuskanci nade-naden kwamishinoni da sauran masu ba shi shawara.

Dalilan da Gwamnan ya bayar na kin nada wadanda suka girme shi don ba su mukami shi ne, “Ni ba zan iya yi wa wadanda suka girme ni tsawa ba, idan na ba su mukami kamar yadda na yi a mulkina na farko,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Zan mayar da hankalina ne wajen zabo matasa masu jini a jika da zan ba su mukamai.”

Haka ya ce, wanda zai nada mukamin Sakataren Gwamnatinsa matashi zai zaba. Tsohuwar Sakatariyar Gwamnatin Jihar,  Tina Agbor ta girmi Gwamnan, haka Mataimakinsa Furofesa Ibara Esu, wanda tsohon malamin jami’a ne a Jami’ar Kalaba, shi ma ya girme shi. Gwamnan a jawabinsa na karbar ragamar jihar wa’adi na biyu ya ce, “A wannan wa’adin ba zai tafi da kwamishinoni 29, da masu rike da mukaman siyasa 600 ba. Wannan karo zan yi aiki ne da matasa masu jini a jika da zan iya yi wa magana yadda idan sun yi kuskure zan gyara musu.”