✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan bar koyarwa ba saboda fim – Saka

Afeez Oyetoro wanda aka fi sani da Saka, wanda kuma ya shahara a bangaren barkwanci fina-finan Kudancin Najeriya wato Nollywood, ya bayyana cewa zai ci…

Afeez Oyetoro wanda aka fi sani da Saka, wanda kuma ya shahara a bangaren barkwanci fina-finan Kudancin Najeriya wato Nollywood, ya bayyana cewa zai ci gaba da aikinsa na koyarwa tare da wasan kwaikwayo.

Saka wanda ya saba fitowa a matsayin dan barwanci a fim, ya fito a fina-finai da dama wadanda suka hada da Wedding Party da kuma Ojukokoro. Sai dai kuma da yawa daga masoyansa ba su da masaniyar cewa shi mutum ne jajirtacce kuma malami mai koyar da wasan kwaikwayo a Kwalejin Adeniran Ogunsanya College of Education da ke Ijanikin ta Jihar Lagos.

Sako ya shaida wa jaridar Punch ta ranar Juma’a cewa duk da cewa masoyansa na son ya bar koyarwa don ya mayar da hankali kan fim, shi kam ba shi da wannan niyyar. A kwanan baya ne dai jarumin ya sauka daga kan matsayin Shugaban Sashen Koyar da Wasan Kwaikwayo na kwalejin.

Saka ya ce, “Babu wani bambanci mai yawa tsakanin koyarwa da harkar fim. Ina kaunar ci gaba da duka biyun. Yayin da kake koyarwa a cikin aji kana yada bayani ne a hukumance. Saboda haka kusan abu daya ne da abin da jarumi ke yi a fim. Jarumin fim nishadantarwa yake yi, a lokaci guda kuma yana isar da sako.

“Ina samun karin ilimi daga aikina na malunta. Yayin da na fita don taka rawa a fim ko a dandali ina kara samun kwarewa sannan kuma ina yin amfani da ita a cikin aji saboda irin wannan kwarewar tana taimakon aikin maluntata.”

Da aka tambaye shi ko mahukuntan kwalejin sun taba yin korafi kan shige da ficensa a matsayinsa na ma’aikaci, sai ya ce ai masu gidan nasa suna da fahimta kuma suna ba wa kowane ma’aikaci damar dogaro da kansa.

“Shugabannin masu kaunar cigaba ne da ke ba ma’aikata damar gina kansu, kuma ba za su yi korafi ba matukar dai abin da muke yi bai ci karo da aikimmu na koyarwa ba. Shi ne dalilin da ya sa nake yin fim a lokutan hutu ko kuma karshen mako. Saboda haka duk lokacin da na fita na dawo ina kara wa aikina na malunta kwarjini.”

Ya kara da cewa, “Ina amfani da lokacina ta hanyar da ta dace, hatta a lokutan da bana cikin aji kodai ina shakatawa a kasar waje ko kuma ina wurin shirya fina-finai.”

Ganin cewa ya samu nasara a harkar fim, jarumin ya nuna sha’awarsa ta shiga wasu harkokin na kashin kansa. “A kwanan nan na fara shirya wani wasan kwaikwayo mai dogon zango da kuma mai gajeran zango. Ina fatan samun goyon baya domin kammaluwarsu badi.”