Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ba zan bayyana sunan wanda zai gaje ni ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ba zai bayyana sunan kowa ba, a matsayin wanda zai gaje shi.

Buhari wanda aka rantsar da shi a ranar 29 ga watan mayu wannan shekara domin sake yin wa’adi na biyu, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar yancin ci gaba a fadar shugaban kasa.

ADVERTISEMENT

Yan kungiyar sun bukaci shugaban da ya fara zaburar da wani matashi, domin ya kasance wanda zai gaje shi, amma Shugaba Buhari y ace dole ne wanda zai gaje shin sai ya jajirce kamar yadda ya yi, ya kara da cewar wanda zai gaje ni ai ya zama abin raha  a gareni, domin idan na yi hakan na jawowa wanda na ambata sunan nasa matsala walau macece ko namiji, don haka ku bari duk wanda yake son ya zama shugaban kasa ya daura damara kamar yadda nayi.

Yace “Ina da yakinin cewar duk wadanda suke da sha’awar zama shugaban kasa sun san gwagwarmayar da nayi har sau 3 ina nema amma sai a karo na 4 Allah ya yi ikonsa, don haka ina ganin ku kara himma wajen gyaran al’amuran kasar nan, domin ci gabanta shine abu mai muhimmanci ga matasa masu tasowa.” Ya ce mafi akasarin matasan mu suna daukar abu cikin sauki, ku duba har sau uku nake tsayawa takarar shugabancin kasa, amma a karshe ina karewa a kotun koli, ku tuna wannan na bukatar sadaukar da kai da kwazon aiki, sai dai mutane na daukar al’amrin da sauki a cewarsa.”

ADVERTISEMENT

A game da harkar ilimi kuwa, Shugaba Buhari cewa ya yi a cikin shekaru hudu an bawa sashin ilimi kudin da yah aura Naira Tiriliyon daya, ta hannun hukumar samar da ilimi bai daya, gidauniyar tallafawa manyan makarantu da suke bukatar tallafa musu, hakazalika an bada Naira Biliyan 25 ga jami’oi domin su biya alawus alawus na malamai.

Haka akan shirin ciyar da dalibai abinci a makarantu wanda yara fiye da miliyan 10 suke amfana wanda hakan ya taimaka wajen sa iyaye tura yaransu zuwa makaranta.

A nasa jawabin Jagoran Tawagar Dr Bolariwa Bolaji cewa ya yi akwai bukatar a tantance makarantu sakandire da na firamare a duk fadin kasar nan, sai ya bukaci shugaban kasa da ya dauki matakai don magance kalubalan da ke fuskantar harkar Almajiranci a kasar nan, ya kuma bukaci shugaban da ya janye lasisin rijiyoyin mai da aka bawa wasu daidaiku a kasar nan.