Ba zan gayyaci ’yan kwallon da ke dumama benci ba – Kocin Eagles

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Gernot Rohr ya ce ba zai sake gayyatar ’yan kwallon da ke dumama benci a kulob din da suke yi wa wasa a sassan duniya ba.

Kocin ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da jaridar SportingLife a ranar Talatar da ta wuce.

Ya ce zai yi haka ne don ganin ’yan wasan da suka fi cancanta ne kawai za su yi wa kungiyar wasannin share fagen zuwa gasar cin Kofin Afirka da kasashen Benin da Lesotho a wannan wata da muke ciki.

Nan da mako biyu masu zuwa ne Kungiyar Super Eagles za ta kece-raini da kasashen Benin da Lesotho a kokarin hayewa gasar cin Kofin Afirka da za a yi a Kamaru a shekarar 2021.

Mai magana da yawun kungiyar Toyin Ibitoye a wata hira da ya yi da manema labarin wasanni ya tabbatar da ikirarin Gernot Rohr na ba zai sake gayyatar ’yan kwallon Eagles da ke dumama benci a kulob dinsu ba.  “Ba mu da lokacin da za mu gwada kwazon ’yan kwallo a yanzu, don lokaci ya kure, don haka za mu tabbatar duk ’yan kwallon da za mu gayyata suna buga wasa a kan kari a kulob dinsu.

ADVERTISEMENT

“Ina tabbatar muku cewa za mu fi mayar da hankali ne wajen gayyatar ’yan kwallon da suka yi mana wasannin sada zumunta da kasashen Ukraine da Brazil a watan jiya sai dai komai zai iya faruwa wajen canja sunayen wadansu daga ciki,” inji shi.

Idan za a tuna Super Eagles ta gama ne a matsayi na uku a gasar cin Kofin Afirka da aka yi a Masar a watan Yunin bana.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya