✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan nemi yin tazarce ba – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da surutan da ya ce ana watsawa da ake danganta shi da yunkurin yin tazarce karo na uku…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi watsi da surutan da ya ce ana watsawa da ake danganta shi da yunkurin yin tazarce karo na uku a shekarar 2023, idan ya kammala zangon mulkinsa na biyu.

Shugaba Buhari ya ce ba zai taba yin tazarce ba, kuma ba ya da wannan niyya a boye a zuciyarsa.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Juma’ar da ta gabata a wurin Taron Kwamitin Zartaswar Jam’iyyar APC  da aka gudanar a Abuja.

“Ba ba zan taba ganganci ko tafka kuskuren neman yin tazarce karo na uku ba. Baya ga doka ta ba ni damar yin zango biyu kadai. Sannan kuma  ga tsufa ya cim min, na kuma rantse da Alkur’ani cewa zan bi ka’idojin da dokar kasa, ta tsara na yin wa’adi biyu a kan mulki. Don haka ba zan karya wannan rantsuwa ba,” inji shi.

Ya ce: “A yanzu tsufa ya kama ni, kuma ina zango na biyu, wanda shi ne na karshe da doka ta amince min. Don haka ba zan yi kuskuren neman zango na uku ba. Ba zan sake neman kuri’ar kowa ba a kasar nan.”

Sai dai duk da wannan kalami na Shugaba Buhari, jama’a da dama ba su amince ba, lura da alkawurran da suka ce ya karya a baya.