✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan roki NFF ta sabunta kwantiragina ba – Rohr

Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles, Gernot Rohr ya ce yana nan yana jiran Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) don jin ko…

Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa, Super Eagles, Gernot Rohr ya ce yana nan yana jiran Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF) don jin ko za ta ba shi sabuwar kwangila ta ci gaba da horar da ’yan wasan Super Eagles din.

Kocin dan kasar Jamus, ana sa ran kwantiraginsa zai kare ne a cikin watan Yuli mai zuwa amma har yanzu babu wata tattaunawa da ta faru tsakaninsa da hukumar kwallon don sabunta kwantiragin nasa.

Rohr ya kai Kungiyar Super Eagles matakin buga gasar Cin Kofin Kwallon Kafa ta Duniya a 2018 da aka yi a kasar Rasha sannan shi ne ya jagoranci kungiyar ta samu matsayi na uku a gasar Cin Kofin Kasashen Afirka da aka yi bara a kasar Masar.

Kocin mai shekara 66 ya ce yana nan yana aikinsa yadda ya kamata amma fa ba zai taba rokon hukumar ta sabunta kwantiraginsa ba.

“Ba zan roki NFF ta sabunta kwantiragina ba. NFF ce ya kamata ta neme ni, kuma ina nan ina jiranta. Abin da ke gabana shi ne in maida hankali kan Super Eagles kuma shi na sanya a gaba,” inji shi.

An shirya Kungiyar Super Eagles dai an shirya za ta kara da kasar Saliyo a Jihar Delta ranar 27 ga wannan wata da muke ciki wanda kuma daga bisani bayan kwana hudu da buga wasan, Super Eagles za ta je can Saliyo su kara karawa. Amma a halin yanzu an dage wannan wasanni saboda barazanar yaduwar cutar Kurona.