Search
Subscribe
Ba zan tanka wa Guardiola ba – Klopp

Ba zan tanka wa Guardiola ba – Klopp

Kocin Liberpool, Jurgen Klopp ya ce ba zai tanka wa takwaransa na Manchester City, Pep Guardiola game da kalamansa kan kungiyar ta Liberpool ba, yayin da za su kara a wasan hamayya jibi Lahadi.

Jurgen Klopp ya yi ikirarin ba zai ce uffan ba game da zargin ‘kwagen wasa’ a martaninsa ga kalaman Kocin Manchester City Pep Guardiola ya yi kwanaki inda ya zargi kan dan wasan Liberpool, Sadio Mane.

Guardiola ya kara haddasa tankiya tsakanin kungiyoyin biyu da ke saman teburin gasar Premier – a yayin da suke shirin karawa jibi Lahdi, inda ya zargi dan wasa Sadio Mane da kwangen faduwa yayin wasa da gangan.

Dan wasan gaban dan kasar Senegal, an hura masa bugun da kai sai mai tsaron gida bayan da ya yi kwangen cewa dan wasan Aston Billa Frederic Guilbert ya ture shi a yayin wasansu ranar Asabar din makon jiya.

Guardiolan ya fada wa shirin labaran wasanni na BBC cewa; “Wasu lokutan yakan fadi a kasa ba tare da an taba shi ba, kuma yana da baiwar cin kwallaye masu ban mamaki ana dab da hura tashi. A gaskiya yana da baiwa.”

Mane dai ya zura kwallon da ta bai wa kungiyarsa nasara saura kiris a tashi wasan; inda suka doke Aston Billa da ci 2-1 – hakan ya bai wa Liberpool damar ci gaba da zama kan teburin Premier da tazarar maki 6 a tsakininsu da Manchester City wanda su ma suka samu nasara a gida da ci 2-1 kan kungiyar Southhampton.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin