✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba zan yi fim din karuwanci ba – Konkona

Fitacciyar jarumar fina-finan Indiya Konkona Sen Sharma ta ce ba za ta yi fim din karuwanci ba. Ta ce: “Ba na so na yi fim…

Jaruma Konkona Sen SharmaFitacciyar jarumar fina-finan Indiya Konkona Sen Sharma ta ce ba za ta yi fim din karuwanci ba.
Ta ce: “Ba na so na yi fim din da zai jawo yamididi a gari, kuma irin wadannan fim din suna daga ciki. Don haka ba na tsammanin zan yi shi.”
Ankush Bhatt shi ne daraktan fim din, wanda yake dauke da labarin da yake nuna karuwanci a Mumbai. Ya ce: “Mun iya bakin kokarinmu don Konkona ta amince amma ta ki. A yanzu dai ban san ko za ta amince ba.”
“Rol din za ta hau za a nuna ta ne daga shekara 16 zuwa 60. Ya kunshi matakai 5. Don haka ne muka dage don ganin mun samu wacce za ta iya, kuma muna da yakinin za ta iya.” Inji shi.
Jaruma Sakshi Tanwar ta za ta hau matakin mai tallafa wa jaruma.
A dangane da fim din sai Bhatt ya ce: “Fim din ba wai a kan tsagwaron karuwanci ba ne, a’a, za mu nuna ayyukan da suke yi da rana ne wurin samun ‘yan kudade. Zai kuma yi bayanin fataucin yara da ‘yan mata. Ba za mu yi wa karuwanci ado ba ne, za mu nuna irin mawuyacin halin da suke samun kansu a ciki ne.”