Search
Subscribe
Ba zan yi takara da Buhari a APC ba – Shekarau

Ba zan yi takara da Buhari a APC ba – Shekarau

Malam Ibrahim ShekarauTsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar ANPP a zaben shekarar 2011, Malam Ibrahim Shekarau ya ce ba zai tsaya takara da Janar Muhammad Buhari a shekarar 2015 karkashin sabuwar Jam’iyyar APC ba.
Bayanin na Shekarau ya zo ne ’yan kwanaki kadan bayan da wasu fitattun shugabannin Arewa suka sasanta sabanin da ke tsakaninsa da Janar din. An rika ruwaito cewa ’yan siyasar biyu da wasu ’yan siyasar Arewa suna yyunkurin tsayawa takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APC wadda ta mika kujerar ga shiyyar Arewa.
Shekarau ya tabbatar wa Aminiya cewa an sasanta takaddamar siyasa da ke tsakaninsa da Janar Buhari, kuma dukkansu sun amince za su yi aiki tare domin cin nasarar sabuwar Jam’iyyar APC.
Shekarau wanda ya yi magana tab akin kakakinsa Malam Sule Ya’u Sule ya ce, bai dauki takarar mukami a matsayin abin ko-amutu-ko-a-yi rai ba, kuma zai karbi duk matsain da Jam’iyyar APC ta ba shi.
Ya shaida wa wakilinmu ta tarho cewa, “Shekarau ya tsaya takarar Shugaban kasa ne a shekarar 2011 saboda suna jam’iyyu daban-daban da Janar Buhari. Yanzu da suke cikin jam’iyya daya ba zai tsaya takara da Janar Buhari ba, saboda yana matukar girmama shi, kuma a shirye yake ya yi biyayya ga duk abin da Janar din zai ce. Ya ce, ba zai tsaya takara ba idan Janar din zai tsaya.”   ‘
Ya tabbatar da ganawar da ta gudana a tsakanin Janar Buhari da Malam Shekarau a Kaduna, inda ya ce a wurin ganawar ’yan siyasar biyu sun amince za su yi aiki tare domin samun nasarar Jam’iyyar APC a kasar nan.
Sabanin siyasa ta shiga tsakanin Janar Buhari da Malam Shekarau ne a shekarar 2005, lokacin da Janar din ya ki halartar gayyatar da Shekarau ya yi masa na ya kaddamar da babura masu taya uku a karkashin shirin A Daidaita Sahu.
Wata majiya ta kusa da ’yan siyasar ta ce, wasu ’yan siyasa da ke kusa da Janar Buhari ne suka rika iza wutar rikicin siyasa a tsakaninsu. “Sun yi ta cika Janar Buhari da karairayi domin raba tsakaninsu. Kuma sun samu nasara, sai dai kuma wadannan mutane a yanzu ba su tare da Janar din.Janar Buhar da kansa ya fadi a kwanakin baya a gidan Rediyon Faransa cewa mutanen da suke kewaye da shi sun yi masa zagon kasa ga kamfe dinsa,” inji majiyar.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin